’Yar bola
“’Yar bola ko ’yar bala’i?” tun karshen makon da ya arce, duk inda mutum ya wilkita a babban birnin Haurobiya, wato Haurubja, babu abin da zai ji gungun mutane na tsokaci a kai kamar cutar ’yar bola. To ka ji GizBaba kada ka dauko wata yarinya ake nufi. Wannan sabuwar cutar da ke jefa firici […]
“’Yar bola ko ’yar bala’i?” tun karshen makon da ya arce, duk inda mutum ya wilkita a babban birnin Haurobiya, wato Haurubja, babu abin da zai ji gungun mutane na tsokaci a kai kamar cutar ’yar bola. To ka ji GizBaba kada ka dauko wata yarinya ake nufi. Wannan sabuwar cutar da ke jefa firici a cikin tunanin al’ummar Yammacin Ifrikiyya, balbalin bala’inta ya watsu a kasashen Labin-bera da Saliyo da Gini. Kuma kasashen duniya wadanda suka hada da kasar Uban-Mama da Sawun-diyyar Larabawa da Hadaddiyar Daular Larabawa duk sun baza na-mujiyarsu wajen bibiyar kadin uwar jikin masu shawagi a tsuntsayen sama; kai kamarin balbalin bala’in ’yar bola, ya sanya an hana wasu Masu fuskantar alkibla don kadaita Mahalicci da ibada sauke farali a bana.
’Yar bola ta shiga bakin duniya, amma duk da haka sai taka rawarta take yi a kan bola. Ni dai na san tafi karfin Baban bola, mai tsince-tsince a kan juji. Ance tana ta cin jemagu da birrai da sauran na’ukan namun daji. Kai ’yar bola tana matukar firgita al’umma. Kuma masana a kullum sai kara jefa wa mutanen Ifrikiyya tsoro suke yi. Kowane yunkuri ake yin a karya lagon ’yar bola?
A kasar Haurobiya dai an tabbatar da cewa wadanda ’yar bola ta kassara ba su wuce mutum kofar hanci ba, har ma da Bokanyar Turai guda. Sannan a kasar Labin-bera da Saliyo da Gini an samu a kalla mutum dari madambaci da madambaci da kwanciyar magirbi. To, wannan dai duk alkaluman kididddiga ne kawai, amma mafi yawancin bala’in ’yar bola da ake da kwakwazo a kansa, a fadin duniya, musamman a Yammacin Ifrikiyya, inda al’amarin ya fi kamari, gama-garin al’umma ne za su jikkata, matukar ba su tashi haikan wajen yi wa tufkar hanci ba. Domin wadanda ke bibiyar cututtukan da suka kassara uwar jikin al’umma a daukacin fadin duniya, musamman a wannan karnin, sun hada da kanjamewa da jemewa da lashe-lashen uwar jiki da tarin fuka, amma duk ba a jefa wa al’umma firgici ba, kamar yadda ake ta kwakwazon ’yar bola.
Ana ta shaci fadi kan yadda za a samar da makaman da za su karya lagon ’yar bola, don kada jikkata Haurobiyawa da sauran al’ummar Ifrikiyya, har ma wasu sun fara baza cewa namijin goriya na da tasirin tokareta. Kai a wata ruwar ma cewa aka yi namijin goriya ya fara yin karanci a kasashen da ’yar bola ke taka rawa.
A daidai lokacin da ake ta tararraddadin balbalin bala’in ’yar bola a Harubja, sai akwai akwatin Magana na Babban Bakin Ce ce ku ce na birnin Lantsandan ya bijiro da wani muhimmin batu kan yadda za a samar da garkuwa da sulken tokare ’Yar bola, don kar taka rawar lallaga uwar jikin al’umma. Kuma Gwamnatin Haurobiya ta umarci wani gungun na kwararrun masanan sarrafa kweayoyi, a karkashin jagoranci Morin Ihu, tsohon Shugaban Hukumar Zabi-sonka, su samar da sulke da garkuwar garkame ’yar bola.
’Yan makarantar Dodorido, ya kamata ku fasko cewa, amfanin sani aiki da shi. Don haka koda Hukumar Kula da Uwar jiki ta Duniya da Gwmanatin kasar Haurobiya ba su yi wani katabus ba, kada mu yi wasararirai, mu dauka za a shawo kan ’yar bola ba tare da mun yunkura wajen ingata muhallinmu ba? Masana sun tabbatar da cewa ’yar bola ta bazu ne daga jikin jemagu da birai. To, me zai hana Ma’aikatar Kula da Uwar jikin al’ummar Haurobiya ta Tarayya, ta fara bin kadin uwar jikin mafarauta da masu dundume kururunsu da naman gwaggon biri da na jemage. Sannan akwai bukatar masu gadin gandun daji su bazama, tare da Bokayen Turai, don kula da uwar jikin zaki da damisa da giwa da barewa da gada da hankaki da balbelu da kurcaccaki.
Haurobiyawa kada ku dauka ko wasanninmu irin na dodanni nike yi, a’a, ko ka dan, domin ina da masaniya kan cewa akwai kuniyoyin al’umma da ke fafutikar kare hakkin dabbobi da tsuntsaye a kasashen duniya, musamman kasar Uban-Mama da Gandun Gandi a nahiyar Asiya. Kai hasali ma akwai masu fafutikar kare hakkin bishiyoyi da sauran tsirrai da ke fuskantar barazana daga ayyukan mutane.
Kafin in karkare batutuwana kan musifar ’yar bola, ya zama dole in tursasa GizBaba ya yi wa ’yan bayajn kango jawabi, kan matakan da suke dauka na shawo kan ’yar bola.
Sanin kowane a kasar Haurobiya cewa tsafta cikon addini ne, a wata fadar ma cewa ake yi wani yanki ne na imani. Lallai mu daina barin tarin bola a cikin gari, don kada ta haddasa mana yaduwar ’yar bola ko mai lashe uwar jiki. Mu yi kokarin raba matsugunnin al’umma da kusu da jaba; mu share gizo-gizon dakin gwagwago mai haifar wa al’umma ciwon tau-tau. Wajibi ne bokayen Turai su tabbatar ana yanka lafiyayyun nagge da balama da raguna lafiyayyu a mahauta.
A daidai lokacin da ake fama da firgicin ‘yar bola a Haurobiya, bokayen Turai na yajin kwadago. Farfajiyar Bokan Turai ta zama kango. Kodayake akwai masu zaman kansu da ke neman kadago. Haurobiyawa mu shiga taitayinmu8, domin bala’in wasu shugabannin Haurobiyan, ya fi balbalin bala’in ‘yar bola. Wannan kuwa duik gaggarumar garabasar dama-dama dakurda-kurdar siyasar Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, wadda ke jan ragamar Haurobiya a tsarin damo-da-kura-da-diyya, tun daga shekara ta alif da manuniyar kasa da ta kasa da ta kasa, har zuwa shekara ta dubu kramin lauje da sili da tsayuwa bisa kafa daya. Kuma wai don bokayen Turai sun tafi yajin kwadago, ina ruwan jiga-jigan mai dan botio da sanda jirge, tunda ai talakawan Haurobiya ne ke zuwa wajensu. Ku sani, su fa farfajiyar koyon watsattsaken ‘ya’yan manyan Haurobiya tana kasashen ketare; Farfajiyar Bokan Turansu tana ketare. Ai kun ga sun ketare wa ‘yar bola ko? Talaka dai shi aka bari da taraddadin balbalin bala’in ‘yar bola.
Lokacin ya yi da jami’an shige da fice a kan iyakokin kasar Haurobiya za su kara matsa kaimi wajen tantance mutanen da ke da shaidar tantance ingancin uwar jiki bakin haure da masu zuwa safara kasashen ketare. Matukar muka dabbaka wadannan dabaru, to cikin yardarm Mai-duka za mu tsira daga gada da rawar ’yar bola. Da zarar mun shawo kan matsalolinmu. To sai mu kai dauki ga sauran kasashen Ifrikiyya da ke fama balbalin bala’in ’yar bola. Mu kuma hada karfi da karfe da kasashen Uban-Mama da Gandun Gandi da kasar Sin don karya lagon ’yar bola.