’Yar fim Bimbo Akinsanya ta yi aure
Bimbo Akinsanya, wacce ta shahara wajen fitowa cikin fina-finan Yarabanci a Kudancin Najeriya ta yi aure.’Yar fim din dai kafin ta kai ga samun wannan dama, an tuhume ta a kwanakin baya da laifin kisan kai, amma bayan an tufka shari’a a Legas sai kotu ta sallame ta, bayan ta samu tabbacin cewa babu hannunta […]

Bimbo Akinsanya, wacce ta shahara wajen fitowa cikin fina-finan Yarabanci a Kudancin Najeriya ta yi aure.
’Yar fim din dai kafin ta kai ga samun wannan dama, an tuhume ta a kwanakin baya da laifin kisan kai, amma bayan an tufka shari’a a Legas sai kotu ta sallame ta, bayan ta samu tabbacin cewa babu hannunta cikin laifin.
Hidindimun auren nata sun faro ne tun makonnin da suka gabata, inda iyayen angon suka gabatar da bukatar dansu a gidan su amarya. An yi kwarya-kwaryan bikin baiko, inda ’yan uwa da abokan arziki suka halarta.
A ranar Asabar, 24 ga watan jiya ne aka gudanar da bikin auren nasu na gargajiya a Legas, inda abokan sana’ar Bimbo, wato ’yan fim da mawakan zamani suka kasance tare da ita a wajen bikin, kamar kuma yadda ’yan uwanta da na ango suka kasance a sahun gaba wajen tafiyar da al’amuran bikin.
A makon jiya ne kuma aka gudanar da bikin auren a zamanance, wanda haka ya kawo karshen zaman gwagwarci ga ’yar fim din.