’Yar fim da ta Musulunta a Indiya ta shirya yin aure

Wata matashiya mai shirya fina-finai a Kudancin Indiya da ake kira Monica ta Musulunta.  Kuma yanzu haka ta yanke shawarar yin aure don ta huta da rayuwar gwagware.“Na yanke shawarar shiga addinin Musulunci ne kawai don na gamsu da ka’adojin addinin ba wai saboda kudi ko don neman suna ba.  Sannan na yanke shawarar daina […]

’Yar fim da ta Musulunta a Indiya ta shirya yin aure
’Yar fim da ta Musulunta a Indiya ta shirya yin aure

Wata matashiya mai shirya fina-finai a Kudancin Indiya da ake kira Monica ta Musulunta.  Kuma yanzu haka ta yanke shawarar yin aure don ta huta da rayuwar gwagware.
“Na yanke shawarar shiga addinin Musulunci ne kawai don na gamsu da ka’adojin addinin ba wai saboda kudi ko don neman suna ba.  Sannan na yanke shawarar daina yin fim da zarar na yi aure don haka ba na tsammanin zan canza wannan shawarar da na yanke.” Inji ta a lokacin da take yi wa manema labarai jawabi.
Ta ce ta kwashe kimanin shekara hudu tana nazarin addinin Musulunci amma sai a wannan lokaci Allah Ya ba ta ikon shiga addinin na Islama. Monica ta kara da cewa mahaifinta Kirista ne, yayin da mahaifiyarta kuma take bin addinin Hindu kuma a lokacin da ta yanke shawarar shiga addinin Islama mahaifanta sun yi maraba da shawararta kuma sun yi mata addu’ar fatan alheri.
Ta ce fim din da ta yi na karshe da ake sa ran kwanan nan zai fito shi ne Nadhigal Nanaibathillai  kuma tana fata shi ne fim din ta na karshe saboda dalilai biyu.  Na farko ta karbi addinin Islama na biyu kuma za ta yi aure.
Asalin sunan da iyayenta suka rada mata shi ne Rekha Maruthiraj amma ta samu Monica ne a wani fim da ta shirya mai suna Tamil and Telugu.  Daga bisani kuma ta sake canza suna zuwa Perbana bayan ta fito a wani fim mai suna Malayalam.  Bayan ta koma Musulma a yanzu sai ta canza sunanta zuwa M.G. Rahima.  Don haka yanzu ta bukaci a rika kiranta da suna Rahima saboda Musuluntar da ta yi.
Ta bayyana labarin Musuluntar ta ne a ranar Juma’ar da ta wuce a wata hira da ta yi da manema labarai a Kudancin Indiya.  Sannan jim kadan bayan hirar ce kuma ta baza hotunanta masu dauke da shiga irin ta matan Musulmi, sanye da hijabi a yanar gizo don tabbatar da ikirarinta ga daukacin duniya.
Monica da yanzu ake kira Rahima ta karbi kyaututtuka da dama a bangaren shirya fina-finai a ciki da wajen Indiya, musamman kyautar da ta karba a fim din da ta shirya mai suna Tamil a watan Nuwamban 2013.
Monica dai ba ita ce ’yar fim ta farko da ta taba Musulunta a Indiya ba.