’Yar fim Ini Edo ta gamu da wulakanci a bikin Glo

Lahadi ta makon jiya ta zo kuma ta wuce sai dai ga shahararrar ’yar fim Ini Edo, rana ce da ba za ta taba mancewa da ita ba a rayuwarta, domin kuwa a ranar ce ta gamu da wulakanci daga masu tsaron kofar shiga gidan wasan tallata kamfanin sadarwa na Glo.Kamar yadda kafar watsa labarun […]

’Yar fim Ini Edo ta gamu da wulakanci a bikin Glo

’Yar fin Ini EdoLahadi ta makon jiya ta zo kuma ta wuce sai dai ga shahararrar ’yar fim Ini Edo, rana ce da ba za ta taba mancewa da ita ba a rayuwarta, domin kuwa a ranar ce ta gamu da wulakanci daga masu tsaron kofar shiga gidan wasan tallata kamfanin sadarwa na Glo.
Kamar yadda kafar watsa labarun al’amuran fim ta intanet, Nigerianfilms.com ta ruwaito, Ini Edo ta ci adon kure adaka, ta isa otel din Oriental Hotel da ke Legas kafin karfe shida na yamma, inda Glo ya gayyace su domin rakashewa.
Cikin ’yan wasan da aka gayyata, ita ce ta farkon hallara, amma masu tsaron kofa suka ce atufau ba za su ba ta wuri ta wuce ba. A cewarsu, ba a ba su izinin su bar kowa ya shiga ba.
Majiyar Aminiya ta shaida cewa, lokacin da ’yar wasan ta samu kanta cikin wannan wulakanci sai ta rasa yadda za ta yi. Haka ta sanya ta koma wajen da ake turke motoci tana ta kiran waya. Haka ta zauna har sai zuwa karfe tara na dare, inda aka ce jaruman fim, RMD da Desmomd Elliot ne suka cece ta, suka kama hannunta, suka shigar da ita zuwa zauren wasan.
Wulakanci na biyu da Ini Edo ta fuskanta, shi ne bayan ta samu shiga zauren wasan. Okey Bakassi ne ya bijiro da wulakancin, inda ya yi ta lissafo jakadun Glo da ke zauren amma ya tsallake sunan jarumar bai ambace ta ba, wacce ita ma jakadiya ce ta musamman ga kamfanin. Sau uku yana tsallakae sunanta, kamar yadda binciken Aminiya ya tabbatar kuma al’amarin ya bata mata rai matuka, fiye ma da wulakancin da aka yi mata a bakin kofa.
Majiyarmu ta ci gaba da cewa, cikin fushi Ini Edo ta dauki jikkarta, ta yi wa kofar tsinke. Haka ta bar zauren wasan cikin kaskanci da wulakanci.
Kadan daga cikin ’yan wasan da suka fantama a wurin bikin nan sun hada da Tuface Idibia da Naeto C. da Pskuare da Burma Boy da Waje da Omawunmi da sauran fitattun ’yan fim din Najeriya.