’Yar fim Jennifer Aniston ta musanta samun cikin shege

Shahararriyar ’yar fim din Amurka, Jennifer Aniston, ta musanta jita-jitar da ake ta yadawa a ’yan kwanakin nan, cewa ta samu cikin shege.Aniston ta karyata jita-jitar, a yayin da ta bayyana gaban jama’a a kasar Australiya, a lokacin da ta kasance daya daga cikin ’yan wasan nuni na ‘Kyale and Jackie O Show.’ Ta ce, […]

’Yar fim Jennifer Aniston ta musanta samun cikin shege

Exclusive… 50840344 Actress Jennifer Aniston arrived on the set of her latest film ìWeíre the Millersî in Wilmington, NC on July 23, 2012. Actress Jennifer Aniston arrived on the set of her latest film ìWeíre the Millersî in Wilmington, NC on July 23, 2012. FameFlynet, Inc – Beverly Hills, CA, USA – +1 (818) 307-4813

Yar fim Jennifer AnistonShahararriyar ’yar fim din Amurka, Jennifer Aniston, ta musanta jita-jitar da ake ta yadawa a ’yan kwanakin nan, cewa ta samu cikin shege.
Aniston ta karyata jita-jitar, a yayin da ta bayyana gaban jama’a a kasar Australiya, a lokacin da ta kasance daya daga cikin ’yan wasan nuni na ‘Kyale and Jackie O Show.’ Ta ce, a iya saninta, babu inda ta samu cikin shege. “Na san dai na kara kiba a ’yan kwanakin nan, wanda dalili ke nan wasu ke zargin cewa ko na samu ciki ne. Wannan ba gaskiya ba ne.” Inji ’yar fim din.
Haka kuma, Aniston ta ce, baya ga jita-jitar cewa tana da ciki, wasu ma sun kwarmata cewa wai a makon gobe ne za a daura mata aure. Nan ma ta ce labarin bai da wani tushe kuma bai da makama. “Babu batun cewa za a daura mani aure makon jiya. Ni kaina a yanzu ne nake jin wannan labari marar tushe.” Inji Jennifer.