’Yar fim Nicollette Sheridan ta maka furodusa a kotu
Nicollette Sheridan, ’yar fim din Amurka da aka fi sani da sunan Edie Britt a cikin shahararren fim din nan na ‘Desperate Housewibes’ a makon jiya ta sake maka furodusoshin fim din kotu a karo na biyu.Tun da farko dai, a 2010 ne ’yar fim din ta shigar da karar shugaaban kamfanonin shirya fina-finai na […]

Nicollette Sheridan, ’yar fim din Amurka da aka fi sani da sunan Edie Britt a cikin shahararren fim din nan na ‘Desperate Housewibes’ a makon jiya ta sake maka furodusoshin fim din kotu a karo na biyu.
Tun da farko dai, a 2010 ne ’yar fim din ta shigar da karar shugaaban kamfanonin shirya fina-finai na ABC da Touchstone da kuma furodusan da ya kirkiro fim din na ‘Desperate Housewibes’ Marc Cherry; inda ta kalubalance su cewa an kore ta daga fitowa cikin fim din ba tare da dalili ba. Haka kuma, a lokacin ta sake shaida wa wa kotu cewa an sallame ta daga fim din ne kawai saboda an yi zargin cewa ta yi musayar magana da daya daga cikin marubuta labarin fim din.
Haka kuma a 2012, bayan an buga shari’a mai zafi, sai wani daga cikin alkalan ya ki amincewa da tsarin tafiyar da shari’ar. daya daga cikin alkalan a birnin Los Angeles ya bayyana cewa, tun farko ya dace ne a yanke hukuncin amincewa da wadanda ake kara, cewa bai kamata a saurari ’yar wasan ba, kasancewar furodusoshin fim din tun da farko ba su sabunta kwantaragin daukar Nicollette ba.
A sabuwar karar da ta shigar a makon jiya, ta nuna rashin amincewa da yadda shari’ar baya ta gudana. A wannan karon, ta nuna cewa akwai sababbin tanade-tanaden shari’a da suka ba ta damar sake maka abokan shari’ar nata kotu. Sai dai a wannan karon ma, ’yar wasan ba ta samu nasara ba, domin kuwa mai shari’a ya ce dole sai ta shigar da sabon koke ga Kwamishinan kwadago da ke birnin California a cikin watanni shida masu zuwa.
Ya zuwa yanzu dai Nicollette ta bi umurnin da aka ba ta, inda a cikin watan nan za a ci gaba da sauraren shari’ar tata.