‘Yar fim Stephaine ta shirya shiga gidan miji

Sunanta Stephaine Chijioke, amma an fi saninta da lakanin ‘Arab Money.’ Ta dade tana fantamawa a harkar fina-finai a Kudancin Najeriya. Ta dade ba ta yi aure ba, amma wannan karon, ga dukkan alamu dabenta ya ji makuba, domin kuwa a yanzu gab take da shiga dakin miji.Kyakkyawar ’yar fim din, tuni ta dade tana […]

‘Yar fim Stephaine ta shirya shiga gidan miji
‘Yar fim Stephaine ta shirya shiga gidan miji

Sunanta Stephaine Chijioke, amma an fi saninta da lakanin ‘Arab Money.’ Ta dade tana fantamawa a harkar fina-finai a Kudancin Najeriya. Ta dade ba ta yi aure ba, amma wannan karon, ga dukkan alamu dabenta ya ji makuba, domin kuwa a yanzu gab take da shiga dakin miji.
Kyakkyawar ’yar fim din, tuni ta dade tana soyayya da wani fitaccen mai harkar fetur, mai suna Frank, wanda ke zaune a Fatakwal.
A yanzu haka Stephaine da take cikin shirya manyan fina-finai, kamar ‘Aso Ebi Girls’ da ‘Bride Prize’ da ‘The Damsels’ da ‘All That Glitters’ da ‘Repented Soul’ da sauransu, wata majiya ta tabbatar wa Aminiya cewa, za ta jingine aikin wasu daga cikin fina-finan, domin ta fuskanci baikon auren nata na gargajiya da za a gudanar a watan gobe. Ana sa ran gudanar da bikin a karamar Hukumar Ngor Okpala da ke Jihar Imo, mahaifarta.