’Yar fim Stephanie Linus ta nuna jinkai ga majinyata 22
Staphanie Linus, ’yar fim a Kudancin Najeriya ta tallafa wa majinyata mata 22 masu fama da cutar yoyon fitsari a Jihar Kuros Riba. An gudanar da aikin tiyata a gare su a karkashin kungiyarta ta ‘Edtended Hands Foundation.’ kungiyar tata ta samu tallafi ne daga hukumomin NNPC da SNEPCO, sannan kuma ta samu tallafin wasu […]

Staphanie Linus, ’yar fim a Kudancin Najeriya ta tallafa wa majinyata mata 22 masu fama da cutar yoyon fitsari a Jihar Kuros Riba. An gudanar da aikin tiyata a gare su a karkashin kungiyarta ta ‘Edtended Hands Foundation.’ kungiyar tata ta samu tallafi ne daga hukumomin NNPC da SNEPCO, sannan kuma ta samu tallafin wasu likitoci daga Ogoja, Jihar Kuros Riba wajen daukar wannan dawainiya.
Kamar yadda rahoto ya tabbatar, kungiyar ta dauki tsawon makonni biyu wajen aikin jinya ga matan, inda kuma aka ba su magani da kula ta musamman har suka samu sauki.
Bayan aikin tiyata da aka yi wa matan kuma kungiyar ta raba kayan aikin tiyata ga asibitocin da aka gudanar da aikin. An yi bikin raba kayan ne a gaban Kwamishinar Jin Dadi Da Walwala ta Jihar Kuros Riba, Barista Patricia Endeley da kuma takwararta ta kungiyar USAID, Dokta Nancy Lowenthul. Wasu daga cikin manyan baki da suka halarci taron sun hada da Dokta Joseph Monehine da Dokta Adamu da kuma Dokta Sa’ad Idris.
Da take bayani game da wannan tallafi da take bayarwa ga mata da raunana, Stephenie ta ce: “Saboda dalilai na jinkai da tausayawa, nakan damu sosai da halin kunci da wasu mata ke fuskanta na cutar yoyon fitsari, don haka zan yi duk iya abin da zan iya domin ci gaba da taimaka musu.”
A yayin da ake gudanar da aikin tiyata da jinyar matan 22, ’yar wasan ta rika zagaya su, tana kallon yadda aikin ke gudana. Hakan ta sanya wasu daga cikin likitocin suka yaba mata, suka bayyana cewa tallafin nata ya kasance mai kawo sauyin rayuwa ga mabukata.
“Hakika, yadda na ga likitocin nan suna aikin tiyata ga matan nan, abin akwai tausayawa. Na ga yadda likitocin ke kokarin aikin saukaka wa matan, wadanda suke rayuwar kunci da dadewa. Na ji dadi sosai da na kasance wacce ta sama wa wadannan mata kafar samun sa’ida daga laulayinsu.” Inji ’yar wasan.
Ta kara da cewa: “Wannan aiki da kungiyata ta fara, ba nan zai tsaya ba. Hasali ma, wannan shi ne mafari kuma za mu ci gaba da wayar da kan jama’a bisa wannan cuta, domin a samu kiyaye ta.”