’Yar Hadeja 01

Wata Bahadeja ce ta je Makka har sau uku amma kawarta ba ta kiran ta da Hajiya sai dai ta kira ta da sunanta na asali. Abin ya dame ta sai rannan ta yi wa kawar tata nasiha, ta ce mata: “Kin ga fa Arafata ukku, jifata ukku amma ba ki ce mani Hajiya, sai […]

’Yar Hadeja 01
’Yar Hadeja 01

Wata Bahadeja ce ta je Makka har sau uku amma kawarta ba ta kiran ta da Hajiya sai dai ta kira ta da sunanta na asali. Abin ya dame ta sai rannan ta yi wa kawar tata nasiha, ta ce mata: “Kin ga fa Arafata ukku, jifata ukku amma ba ki ce mani Hajiya, sai dai ki kira ni da ’Yar Hadeja. To, ki ji tsoron Allah, ki tuba ki daina. Kina halaka kanki ne ba ki sani ba, kada ki mutu ki ci wuta. Ke ba ki kirana da Hajiya, yanzu ranar gobe kiyama ina za ki da wannan zunubin?
Daga Amiru Isah Bakori, 07068147933

Mai intabiyu
Wani mutumi ne ana kiransa Tanimu, ya je intabiyu ya bi layi, sai aka kira na gabansa aka fara yi masa tambayoyi kamar haka: “Mene ne sunan shugaban kasarka wanda ya bar gado?” Ya ce: “Goodluck Jonathan.” Wace shekara Janar Murtala Muhammad ya yi mulki?” Ya ce: “1976.” Shin cutar kanjamau tana da magani?” Ya ce: “E, amma likitoci ba su tabbatar ba.” Sai mai tambayar ya ce masa: “Kira mai bi maka.” Tanimu ya fara jin tsoro. Mutumin na fitowa sai ya ce masa: “Don Allah fada mani amsar tambayar.” Mutumin ya ce masa ai ba irinta za a yi maka ba.” Ya ce ya dai fada masa haka nan. Suna kan haka sai mai intabiyu ya ce: “Mutum na gaba ya shigo.” Sai mutumin ya ce wa Tanimu: “Amsar ita ce Goodluck Jonathan, 1976 da kuma E, amma likitoci ba su tabbatar ba. Tanimu ya shiga aka fara tambayarsa kamar haka: “Ya sunanka?” Ya ce: “Goodluck Jonathan.” “Shekarunka nawa?” Ya ce: 1976.” Mai intabiyu ya ji haushi ya ce masa: “Kai mahaukaci ne?” Tanimu ya amsa da cewa: “E, amma likitoci ba su tabbatar ba.”
Daga Nura S. Suleja, 08107575716

Buzu da dankali
Wusu mutane ne suka kira mai sayar da dankali suka saya, sai suka ba Buzu dandano. Da ya ci dankali ya ji dadi, sai ya ce: “A she abin ga dadi aggare shi? Kyan abin ga ka bida kasuwa ka bido shi, ka kawo ga matanka ta dafa ma. Sai ka bari sai can cikin dare kai ta bidan abinka ga duhu abokin hirarka bai sani ba.”
Daga Shehu Muhammad Raga, Azare

Rakumin Buzu
Wani Buzu ne bai taba zuwa birni ba sai abokansa suka ce masa ya shirya su je birni. Suna tafiya a kan rakuma sai mota ta wuce, kafin ya ankara ta bace. Sai ya tambayi wani daga cikinsu cewa wane irin mai ake zuba mata take gudu haka? Aka gaya masa cewa wani irin mai ne idan muka je zai nuna masa. Da suka isa masauki aka daure rakuma sai abokinsa ya ja hannunsa suka shiga gari. Da zuwansu sai ya nuna masa gidan mai, shi kuwa ya je ya taho da rakumisa; ya je ya samu mai ba da mai ya tambaye shi cewa: “Rakumi zai sha lita nawa?” Mai ba da mai ya ce: “A ina za a zuba?” Ya ce a duburar rakumin. Ya ce masa ai ba a zuba wa rakumi mai. Buzu ya ce: “Kar ka raina mini hankali!” Nan aka daga jelar rakumi aka matsa masa fetur. Da rakumi ya ji sabon abu a cikinsa, sai ya kwace daga hunun Buzu, ya fita da gudu, ya yi arewa. Buzu ya yi ta yi wa rakumi tsawa don ya tsawa amma ya ki tsayawa. Buzu kwabe wandonsa ya ce wa mai sayar da mai: “Zuba mini lita biyu in bi rakumina.”
Daga Azzubair M Fagge