’Yar kasar Faransa mai shekara 14 ta haddace Alkur’ani cikin wata 4 a Zariya

Dalibar da ta rika haddace shafi takwas na Alkur’ani a kullum.

’Yar kasar Faransa mai shekara 14 ta haddace Alkur’ani cikin wata 4 a Zariya

Wata yarinya mai shekara 14 ’yar asalin kasar Faransa, Hafizah Fatima Musa, ta kafa tarihi wajen haddace Alkur’ani mai girma cikin wata hudu, a makarantar Nurul Tilawah da ke Zariya a Jihar Kaduna.

Dalibar ta kafa tarihi ne wanda yake da wuya a samu wanda ya haddace Alkur’ani cikin kankanin lokaci kamar wannan,  musamman la’akari da yanayin shekarunta.

Fatima, wadda aka haifa a kasar Faransa sun dawo Najeriya ita da ’yar uwarta, Anljou Musa mai shekara 18 a duniya, don neman ilimin addini, wanda hakan ne ya sa aka sanya su a makarantar Islamiyyar don samun haddar Alkur’anin.

Makarantar wadda ta ke a yankin Gonar Ganye a Zariya, wanda mai ba wa tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan shawara, Tahir Umar Tahir, ya gina, ta kware wajen ba wa dalibai daga kasashen Afirka da Turai horo kan ilimi.

Daraktan makarantar, Nura Umar Tahir, ya ce tun bayan kafa makarantar shekara 25 da suka gabata, ba a taba samun dalibin da ya kafa irin wannan tarihin ba.

“Abu ne mai wuya a duk fadin duniya a samu yarinya mai karancin shekaru a ce ta haddace Alkur’ani cikin shekara hudu ma.

“Fatima daliba ce mai cike da hazaka da fasaha, ko yaushe tunaninta shi ne yin tambaya game da abin da ya shafi ilimi.

“Ta na son yin tambayoyi, idan aka ba ta amsa za ta kara yin wata tambayar ne, wasu tambayoyin ma sun fi karfin shekarunta,” a cewarsa.

Tahir ya ce da farko dalibar ta fara haddace shafi shida na Alkur’ani ne a kullum, lokacin da aka sanya ta a makarantar a watan Satumban 2022, amma daga bisani ta koma haddace shafi takwas a kullum, wanda sauran dalibai sun fi yin haddar shafi biyu zuwa uku.

Kazalika, daraktan ya kara da cewa ’yar uwarta (Anljou Musa) da aka sanya makarantar a lokaci daya ta samu damar haddace iya izu 20 ne zuwa yanzu, yayin da kuma Fatima ta haddace Alkur’anin baki daya cikin wata hudu kacal da fara karatu a makarantar.