’Yar kasar Sweden ta kirkiro agogo mai mari
Wata mata ’yar kasar Sweden ta kirkiro agogo mai mari, saboda haka sai mutum ya yi nazari kafin ya yi amfani da wannan sabuwar kirkirar tata, musamman idan yana da nauyin barci.Simone Giertz ta kirkiro agogonta mai tayar da mutum daga barci da ta lika masa hannun roba da ke marin mutum har sai ya […]
Wata mata ’yar kasar Sweden ta kirkiro agogo mai mari, saboda haka sai mutum ya yi nazari kafin ya yi amfani da wannan sabuwar kirkirar tata, musamman idan yana da nauyin barci.
Simone Giertz ta kirkiro agogonta mai tayar da mutum daga barci da ta lika masa hannun roba da ke marin mutum har sai ya wartsake. Kuma an nuna hotunan bidyonsa da yadda ake amfani da shi ga miliyoyin mutanen da ke mu’amala da shi a shafin sadarwar Youtube.
A bidiyon Giertz ta ce, “an samar da agogon tashi daga barcin ne don kada mutum ya yi ta holewa da jin dadin barci.” Don haka ta yi amfani da hannayen robar wasannin tashe, ta sauya musu fasali wajen lika wa agogon. Ta ce agogon an samu nasarar kirkiro shi ne, ta yadda zai tursasa mutum ya mike daga kwanciyar barci.
Masu mu’amala da shafukan sadarwa na kasar Sin sun bayyana fahimtarsu game da wannan sabuwar kirkira na agogo mai mari. A cewar Boss, me ya sa kake makara? To na tausaya maka, saboda haka akwai takaddama tsakaninka da agogo mai mari,” kamar yadda yake kunshe a shafin twitar @caimin da ke shafin weibo na kasar Sin.
Shi ma wani mai sharhin cewa: “Kamar wannan agogo ya fi dacewa da mutane da ke da gajeren gashi ko masu sanko,” kamar yadda yake kunshe a shafin @haodesuanpanmei na twitter, inda aka kara da cewa mutanen da ke da tsawon gashi, gashinsu zai kanannade.