’Yar kunar bakin wake ta hallaka mutum 12 a Yobe

Wata ’yar kunar bakin wake da ake zargin ’yar kungiyar Boko Haram ne ta hallaka mutum 12 tare da jikkata akalla mutum 60 a harin da ta kai a cikin babbar tashar motar garin Damaturu a Jihar Yobe. ’Yar kunar bakin waken ta kai harin ne da misalin karfe 11.45 na safe a ranar Lahadi […]

’Yar kunar bakin wake ta hallaka mutum 12 a Yobe
’Yar kunar bakin wake ta hallaka mutum 12 a Yobe

Wata ’yar kunar bakin wake da ake zargin ’yar kungiyar Boko Haram ne ta hallaka mutum 12 tare da jikkata akalla mutum 60 a harin da ta kai a cikin babbar tashar motar garin Damaturu a Jihar Yobe. ’Yar kunar bakin waken ta kai harin ne da misalin karfe 11.45 na safe a ranar Lahadi da kasuwar garin ke ci.

Wakilin Aminiya wanda ganau ne kan wannan hari da ya auku yana cikin tashar ya ce lokacin da bam din ya tashi duk cikin tashar ya turnuke da hayaki bayan kara mai karfi lamarin da ya sa mutane suka watse inda daga baya aka gano gawar ’yar kunar bakin waken kanta a rabe da gangar jikinta.
Wakilinmu ya ce a lokacin jami’an tsaro da dama da suka je sayayya suna cikin tashar a lokacin da ’yar kunar bakin waken ta tada bam din, ganin haka ya sa wasu matasa suka rik zargin cewa ’yar kunar bakin wake na da nasaba da jami’an tsaron, inda nan take matasan suka yi ca a kan jami’an tsaron suna zarginsu kan aukuwar harin, kafin wasu ’yan banga da wani jami’in tsaro su kai musu dauki.
Shugaban kungiyar Direbobi ta kasa (NURTW) reshen Jihar Yobe Alhaji Hussaini Ibrahim ya bayyana harin da wani babban abin bakin ciki, kuma ya yi kira ga al’umma su rika hakuri da duk irin binciken da za a yi musu in sun zo shiga tashar. Ya ce ’yar kunar bakin wake ta shammaci masu bincike ne ta shiga tashar.
daya daga cikin wadanda hari ya rutsa da su Malam Kamilu Mai Kayan Miya ya ce, kawai ya gan shi ne a asibiti mutane na kansa, bayan bam din ya tashi a tashar.
Gwamnatin jihar ta bakin Kakakin Gwamna Ibrahim Gaidam Malam Abdullahi Bego ta yi Allah wadai da harin, inda ta yi ta’aiyya tare da jajanta wa ’yan uwan wadanda suka rasu ko suka samu raunuka, tare da umartar asibitocin jihar su ba da magunguna kyauta ga wadanda suka jikkata.