’Yar kwallon Falcons ta nemi Shugaba Jonathan ya cika alkawarin da ya yi musu

’Yar kwallon gaba a kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Falcons Stella Mbachu ta nemi shugaban kasa mai barin gado Goodluck Ebele Jonathan da ya yi wa Allah ya cika alkawarin da ya yi musu na karrama su bayan sun lashe gasar cin kofin Afirka na mata (AWC) da ya gudana a Namibiya klimanin watanni […]

’Yar kwallon Falcons ta nemi Shugaba Jonathan ya cika alkawarin da ya yi musu
’Yar kwallon Falcons ta nemi Shugaba Jonathan ya cika alkawarin da ya yi musu

’Yar kwallon gaba a kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Falcons Stella Mbachu ta nemi shugaban kasa mai barin gado Goodluck Ebele Jonathan da ya yi wa Allah ya cika alkawarin da ya yi musu na karrama su bayan sun lashe gasar cin kofin Afirka na mata (AWC) da ya gudana a Namibiya klimanin watanni bakwai da suka gabata.

Stella ta ce suna yi wa shugaban tuni ne a kan alkawarin da ya yi musu na karramasu bayan sun lashe kofin a karo na bakwai a jere bayan sun lallasa Kamaru da ci 2-0 a wasan karshe.
“Abin bakin ciki ne yadda kimanin watanni bakwai kenan da yin wannan alkawari da shugaba mai barin gado ya yi musu amma ga shi saura kwanaki bakwai suka rage masa a kan karagar mulki amma bai cika alkawarin da ya yi musu ba. Ta ce muddin ya sauka bai karrama su ba ko shakka babu zai sa gwiwoyin ’yan kwallon Falcons da za su fafafata a gasar cin kofin kwallon kafa na mata na duniya da za a fara kwanan nan a Kanada ta yi sanyi saboda tunanin ko da sun nuna kwazo gwamnati ba za ta karrama su ba”.
Sai dai rahotanni sun nuna Shugaba Jonathan ya sanya lokuta da dama don ya karrama ’yan kwallon Falcons amma saboda rashin samun isasshen lokacin da zai yi haka ne ta sa kawo yanzu ya kasa karrama ’yan kwallon.
kungiyar Falcons dai za ta fafata ne a rukunin D da kasashen Amurka da Sweden da kuma na Australia a gasar cin kofin duniya na mata da za a fara a ranar 30 ga watan nan a Kanada.