’Yar kwallon Najeriya Asisat Oshoala ce aka zaba Gwarzuwar ’Yar kwallon Mata Ta Duniya ta bana

’Yar kwallon Najeriya da yanzu haka ke buga wa kulob din Liberpool a bangaren mata da ke Ingila Asisat Oshola ta zama Gwarzuwar ’yar kwallon Duniya (Women Footballer of Year Award) a bangaren mata a bana. Wannan shi ne karon farko da ’yar kwallon Super Falcons din ta lashe gasar. Kuma ita ce gasa ta […]

’Yar kwallon Najeriya Asisat Oshoala ce aka zaba Gwarzuwar ’Yar kwallon Mata Ta Duniya ta bana
’Yar kwallon Najeriya Asisat Oshoala ce aka zaba Gwarzuwar ’Yar kwallon Mata Ta Duniya ta bana

’Yar kwallon Najeriya da yanzu haka ke buga wa kulob din Liberpool a bangaren mata da ke Ingila Asisat Oshola ta zama Gwarzuwar ’yar kwallon Duniya (Women Footballer of Year Award) a bangaren mata a bana.

Wannan shi ne karon farko da ’yar kwallon Super Falcons din ta lashe gasar. Kuma ita ce gasa ta farko da kafar watsa labarai na BBC ya taba shiryawa a bangaren mata. Kenan, za a iya cewa ita ce mace ta farko da ta fara lashe kyautar a tarihi.
’Yar kimanin shekara20, Asisat Oshoala ta doke ’yan kwallon mata da suka fafata a gasar ce da suka hada da ’yar Sifen beronica Bokuete da Nadine Kesler ’yar Jamus da ’yar Sukotlan Kim Little da kuma ’yar kwallon Brazil Marta.
Ta gode wa gidan rediyon BBC a kan wannan zabe da magoya bayanta da kuma masu sararo suka yi mata inda ta jaddada cewa ko shakka babu yin haka zai kara wa matasan da ke tafe kwarin gwiwar cigaba da nuna kwazo musamman a Nahiyar Afirka da kuma a Najeriya.
A kowace shekara ce gidan rediyon BBC zai cigaba da shirya irin wannan gasa a bangaren ’yan kwallon kafa na mata kamar yadda Hukumar FIFA take gudanar da na bangaren maza a duk shekara.
Oshoala dai tana daga cikin ’yan kwallon Najeriya Super Falcons da aka gayyato wadanda za su fafata a gasar cin kofin duniya na kwallon kafar mata da za a fara a ranar Asabar ta makon gode a Kanada.