’Yar kwallon Najeriya Asisat Oshoala za ta koma Arsenal
Rahotannin da ke fitowa sun nuna shahararriyar ’yar kwallon Najeriya da ke buga wa kulob din Liberpool na mata na Ingila Asisat Oshoala ta fara yunkurin komawa kulob din Arsenal na mata da ke Landan.’Yar kwallon ta bayyana haka ne a lokacin da take jawabi a wajen wani taro da hukumar shirya kwallon kafa ta […]
Rahotannin da ke fitowa sun nuna shahararriyar ’yar kwallon Najeriya da ke buga wa kulob din Liberpool na mata na Ingila Asisat Oshoala ta fara yunkurin komawa kulob din Arsenal na mata da ke Landan.
’Yar kwallon ta bayyana haka ne a lokacin da take jawabi a wajen wani taro da hukumar shirya kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta shirya a ranar Litinin da ta gabata a hedkwatar hukumar da ke Zurich na Suwizilan.
’Yar kimanin shekara 21 Asisat ta samu nasarar komawa kulob din Liberpool na mata ne a watan Janairun 2015 daga kulob din Ribers Angels na Najeriya.
Idan za a tuna Asisat ce ta kasance Gwarzuwar ’yar kwallon Afirka ta BBC a bara kuma ta karbi kyautar ’yar kwallon da ta fi nuna kwazo a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na mata da aka yi a shekarar 2014.
Ana sa ran nan da ’yan kwanaki ne ’yar kwallon za ta rattaba hannu a kulob din Arsenal na mata, bayan ta shaida cewa tuni ta samu takardar izinin zama a Landan (Work permit).