’Yar majalisa Elizabeth ta gode wa al’ummar Arewa
Elizabeth Uyinmwen Atibie, daya daga cikin ’yan siyasa mata na jam’iyyar APC kuma ’yar majalisar jiha da aka zaba, ta gode wa al’ummar Hausawa na Jihar Edo kuma ta nemi da su ci gaba da goya wa jam’iyyar tasu baya da hadin kai, domin a cewarta, “da hadin kanku ne za mu samu damar cika […]
Elizabeth Uyinmwen Atibie, daya daga cikin ’yan siyasa mata na jam’iyyar APC kuma ’yar majalisar jiha da aka zaba, ta gode wa al’ummar Hausawa na Jihar Edo kuma ta nemi da su ci gaba da goya wa jam’iyyar tasu baya da hadin kai, domin a cewarta, “da hadin kanku ne za mu samu damar cika muku alkawarin da muka yi muku da yardarm Allah. Ina tabbatar muku cewa, idan na shiga ofis na fara aiki duk wadannan matsaloli da kuke gani kuke fama a ciki to lallai warware su abu ne mai sauki.”
“Tsaftataccen ruwan sha da na yi muku alkawari da kuma wutar lantarki da gyara muku wannan hanya, duk gwamnatinmu za ta yi muku. Kamar yadda kuka sani, NNDC da take a hannun PDP, ta dawo a hannun maigidanmu kuma Shugaban kasa, Janar Muhammadu Buhari. Saboda haka kun gani mu ne za mu gaya masa abin da muke bukata da kuma irin matsalolin da ke damun jama’armu a nan jihar.” Inji ta.
Ta ci gaba da cewa: “A saninku ne, mafiya yawan kamfanoni a kasar nan sun rigaya sun durkushe saboda lalacewar bangaren hukumar wutar lantarki ta kasa. Sai dai yanzu kam gwamnatinmu za ta yi tsayin daka ta ga ta gyara komai, domin amfanin al’ummar Najeriya; tun da mun samu jam’iyyar APC take mulki a matakin Tarayya da nan Jihar Edo. Kun ga magance matsalolin zai zo da sauki. Nan da lokaci kadan a nan gaba wadannan matsaloli da kuke gani za su zama tarihi.”
’Yar majalisa Elizabeth Atibie ta karkare da gode wa daukacin al’ummar jihar, musamman ’yan Arewa mazauna jihar. Ta ce: “Na gode muku da kokari irin wanda kuka nuna a wannan zaben. Allah Ya saka da alheri.”