’Yar Najeriya ta kirkiro manhajar magance batan yara
A koyaushe yara na bata in sun fita yawo, hakan yana ta da hanakalin iyayensu. Sai dai wata ’yar Najeriya Tomisin Ogunnubi mai shekara 14 ta samo mafita. Ogunnubi ta kirkiro wata manhaja ta wayar salula da za ta nuna inda mutum yake. Ana kiran ta “my locator,” kuma an sauke ta fiye da sau […]
A koyaushe yara na bata in sun fita yawo, hakan yana ta da hanakalin iyayensu. Sai dai wata ’yar Najeriya Tomisin Ogunnubi mai shekara 14 ta samo mafita.
Ogunnubi ta kirkiro wata manhaja ta wayar salula da za ta nuna inda mutum yake. Ana kiran ta “my locator,” kuma an sauke ta fiye da sau dubu daya.
Tomisin Ogunnubi na karatu a makarantar sakandaren mata ta bibian Fowler Memorial, Oregun da ke Ikeja a Jihar Legas ce
Wannan labari na daga cikin shirin BBC na masu fasahar kirkira wato BBC Innobators, wanda Gidauniyar Bill da Melinda Gates ta dauki nauyi.