’Yar Najeriya ta yi fice a ayyukan zane-zane a Amurka
Wata ’yar Najeriya mai shekara 16 mai suna Rabi’at Ladan ta samu zamowa daya daga cikin dalibai 26 da Uwargidan Gwamnan Jihar Maryland da ke Amurka, Misis Yumi Hogan ta karrama. Yarinyar wadda ta je Amurka tare da mahaifanta shekara 3 da suka gabata, tana cikin daliban makarantun firamare da sakandare a Jihar Maryland da […]

Wata ’yar Najeriya mai shekara 16 mai suna Rabi’at Ladan ta samu zamowa daya daga cikin dalibai 26 da Uwargidan Gwamnan Jihar Maryland da ke Amurka, Misis Yumi Hogan ta karrama.
Yarinyar wadda ta je Amurka tare da mahaifanta shekara 3 da suka gabata, tana cikin daliban makarantun firamare da sakandare a Jihar Maryland da suka shiga gasar ce sakamakon zaben wasu daga cikin ayyukanta na zane-zane da Uwargidan Gwamnan ke daukar dawainiyar karramawa ga wadanda zanensu ya yi fice.
Akwai dubban makarantun firamare da sakandare a jihar kuma dukan makarantun sun gabatar da ayyukan dalibansu don shiga gasar.
An zakulo 26 daga cikin dubban da aka gabatar da ayyukansu ne bayan an kwashe watanni ana tantancewa kamar yadda daya daga cikin wadanda suka yi aikin tantancewar Mista James Shindle ya shaida wa wakilin Aminiya.
Rabi’at ce kadai bakar fata ’yar Afirka da ta samu nasara a gasar, kuma Mista Shindle ya shaida wa wakilinmu cewa: “Duk wanda ka ga ya samu nasara to kwazonsa ne ya ba shi domin wadanda suka ta ce wadannan hotuna kwararru ne a wannan fanni wadasunmu mun dade muna koyar da darasin zane-zane.”
Ya ce an bi matakai kafin a kai ga tace 26 daga cikin dubban daliban da suka gabatar da ayyukansu. “Idan ka dubi yawan makarantun firamare da na sakandaren ka san duk wanda ya samu isowa nan ya cancanci yabo,” inji shi.
Ita kuwa Uwargidan Gwamnan, Misis Yumi Hogan da wakilin Aminiya ya tambaye ta yaushe ta fara wannan biki na karrama daliban kuma me ya sa sai darasin jan hoto ko zane-zane? Sai ta ce: “Wannan ne karo na 3 da na shirya wannan biki, kuma abin da ya sa na zabi darasin zane-zane shi ne tun ina karama nake sha’awar jan hoto, kuma zan ci gaba da wannan ko da na bar gidan gwamnatin.”
Rabi’at, wadda ‘yar asalin garin Kwantagora ce a jihar Neja, ta shaida wa Aminiya cewa: “Ina cike da farin ciki kuma wannan zai kara mini kwarin gwiwa kan wannan aikin da na sa a gaba, domin duk abin da kake son yi ka dauke shi da muhimmaci.”
Ta ce tun tana gida Najeriya take sha’awar harkokin zane-zane, amma da ta zo Amurka sai ta gane cewa mafarkinta na iya zamowa gaskiya, kuma wannan shi ne abin da take tunanin yi a digirinta ta fannin kwamfuta.
Yanzu haka an lillika wadannan hotuna a gidan Gwamnatin Jihar Maryland, inda za su ci gaba da kasancewa na tsawon shekara daya kafin a canza su da wadanda za su biyo bayansu.