’Yar Najeriya ta zama bakar fatar da ta fi kudi a duniya

Fitacciyar ’yar kasuwan nan da ke zaune a Jihar Legas, Folorunsho Alakija ta zama mace bakar fatar da ta fi kudi a duniya, kamar yadda jaridar kasuwanci ta bentures Africa ta bayyana.  ’Yar kasuwar ta dara wadda take rike da kambun ne wato ’yar jaridar nan Ba’amurkiya, Oprah Winfrey da Dala miliyan 500. Rahoton ya […]

’Yar Najeriya ta zama bakar fatar da ta fi kudi a duniya

‘Yar Najeriya Folorunsho Alakija Fitacciyar ’yar kasuwan nan da ke zaune a Jihar Legas, Folorunsho Alakija ta zama mace bakar fatar da ta fi kudi a duniya, kamar yadda jaridar kasuwanci ta bentures Africa ta bayyana. 

’Yar kasuwar ta dara wadda take rike da kambun ne wato ’yar jaridar nan Ba’amurkiya, Oprah Winfrey da Dala miliyan 500. Rahoton ya ce Misis Folorunsho ta mallaki akalla Dala biliyan uku da miliyan 300. Yayin da Oprah ta zama ta biyu da Dala biliyan biyu da miliyan 700, kamar yadda mujallar Forbes Magazine ta bayyana a karshen watan jiya.
Misis Folorunsho ta fara aiki ne a matsayin sakatariya a wani banki a kasar nan, kafin daga bisani ta shiga harkar man fetur da kafa kamfanin kayayyakin ado da kwalliya. Hakan ba ya rasa nasaba da karatun da ta yi a kasar Ingila a shekarar 1980, inda ta yi nazarinta a fanin ado da kwalliya.
Attajirar mai shekara 62, ta samu lasisin hako man fetur daga gwamnatin tarayya a fadin filin da ya kai murabba’in dubu 617 na man fetur. Kuma an ruwaito cewa kadarorinta sun hada da jirgin saman hawa da farashinsa ya kai Dala miliyan 46 da hajar da ta tasamma Dala miliyan 100. Rahoton ya kara da cewa: “Ba za a iya fahimtar ko akwai bashin da ake bin kamfanin man ta na Famfa Oil ba ko kuma aá, amma duk yadda ta kaya ko debe rabin abin da ta mallaka aka yi, Folorunsho za ta shige gaban Oprah, kamar yadda mujallar Forbes Magazine ta bayyana.”