’Yar sanda ta kashe dan uwanta a rikicin gado
Jami’ar dan sanda ta shiga hannun saboda kashe dan uwanta a rikicin gadon mahaifinsu.
Wata jami’ar dan sanda ta shi hannun kan hada baki tare da kashe dan uwanta a rikicin gadon da mahaifinsu ya rasu ya bari.
Ana zargin jami’ar dan sandan ta taimaka wa ’yan uwanta ne suka aika babban wan nasu lahira domin su ci kasonsa na gdon mahaifin nasu.
- ’Yan bindiga sun kai hari a barikin soja da ke Jaji
- Na rabu da mai neman aurena kan raina Kwankwaso —Budurwa
- Yadda malaman Birnin Gwari suka tsere daga hannun ’yan bindiga
- Yadda na sauya akalar marigayi Ibro –Falalau Dorayi
Kakakin ’yan sandan Jihar Imo, Orlando Ikeokwu, ya ce, “Muna tsare da ita tare da dan uwan nata da ya buga masa faskare.”
Shaidu sun ce matar da saura ’yan uwanta sun lakada wa babban wan nasu duka ne a lokacin da ’yan uwan mahaifiyarsu suka jagorantar tattaunawa kan rabon gadon.
Ana cikin haka ne fada ya kaure tsakanin mamacin da kanen nasa, wani kaninsu ya dauko faskare ya rafka masa a keya, nan take ya fadi magashiyyan, da likitoci suka tabbatar rai ya yi halinsa, sai suka cika bujensu da iska.
Sun kuma bayyana cewa ’yar uwar mamacin, wadda jami’ar dan sanda ce, ta lakada wa mai juna biyun duka.
Shugaban al’ummar ta ke Karamar Hukumar Owerri ta Yamma a Jihar Imo, Martin Daniel, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba.
Amma kakakin ’yan sandan ya ce, “Mamacin ne ya dauko wuka yana barazanar kashe mahaifiyarsu. Ita kuma ’yar uwarsu wadda ’yar sanda ce ta kirawo ’yan uwanta maza su biyu.
“Da zuwansu sai suka fara dambe, daya daga cikisu ya je ya dauko ice ya buga masa, ya fadi bai san inda yake ba; Da kaka kai shi Babban Asibitin Tarayya da ke Owerri, likitoci suka tabbatar da cewa ya rasu.”