’Yar Saudiyya ta bude maciyar abincin mata zalla
Wata mata ’yar Saudiyya ta bude maciyar abincin mata zalla a yankin al-Ahsa. Mai maciyar abincin, wadda ke kiran kanta Al-Sheikha ta ce ta gaji basirar sarrafa girke-girken abinci daga mahaifiyarta.“Mutane na kiran mahaifiyata da Al-Sheikha saboda kwarewar wajen sarrafa girkin abinci a dakin girki. Yanzu tunda na gaji irin baiwarta, kuma na bude wajen […]
Wata mata ’yar Saudiyya ta bude maciyar abincin mata zalla a yankin al-Ahsa. Mai maciyar abincin, wadda ke kiran kanta Al-Sheikha ta ce ta gaji basirar sarrafa girke-girken abinci daga mahaifiyarta.
“Mutane na kiran mahaifiyata da Al-Sheikha saboda kwarewar wajen sarrafa girkin abinci a dakin girki. Yanzu tunda na gaji irin baiwarta, kuma na bude wajen cin abinci nawa, ina son mutane su rika kirana da “Al-Sheikha kamar ita. Da na dan yi jim kadan wajen bude maciyar abincin, amma iyalaina suka karfafa mini gwiwa,” inji shi.
Al-Sheikha, ta ce, ta saba da aikin girki tun yarintarta.
“A da ina yin girki ne kawai ga iyalaina da kawaye na, amma yanzu ga dimbin jam’ar da ke Al-ahsa. Domin na samu kwarewar girki tun ina makarantar Sakandire, inda na rika yin girki a lokutan bukukuwa,” a cewar Al-Sheikha.
Ta ce, ta bude shafin facebook, inda ta rika hulda da abokan ciniki. Sannan ta bayyana yadda ta cin ma burinta
Ta ce ta je cibiyar kasuwanci da masana’ntu, inda ta samu lasisin bude maciyar abincinta
“?Na cimma burina, kuma ina godiya ga ahlina da suka karfaf amini gwiwa. Sannan ina godiya ga dimbin masu sayen abincina, wadanda kan yaba mini tare da suka mai ma’ana,” inji ta.
A kokarinta na kwarerwa a harkar kasuwanci ta yi karatu a makarantar koyon kasuwanci, don sanin dabarun fadada kasuwancinta. “anan na gabatar da manufar bude madafar abinci da zarar na kammala karatuna,” injita.
A cewarta, karatun da ta yi ta samu babban yabo a cikin mutum 28 da suka gabatar da tsarin kasuwancinsu.
“Na kuduri aniyar bude maciyar abinci. Kuma nufina ta kasance ta mata zalla, mai dauke da dakin girki da zan yi amfani da shi wajen karfafa wa mata gwiwa, musamman masu sha’awar girke-girke, ta yadda za su koyi wani abu daga basirata. Sannan ina son mayar da hankalina kan abincin gargajiya da ake ci a wannan yankin na Al-Ahsa,” inji Sheikha.