’Yar Shaikh Ibrahim Nyass ta rasu
Sayyada Maryam Nyass ta sadaukar da rayuwarta kacokan wurin hidimar Alkur’ani
Allah Ya yi wa Sayyada Maryam Shaikh Ibrahim Inyass rasuwa a Kasar Senegal.
Sayyada Maryam diya ce ga shahararen malamin Musulunci na duniya kuma jagoran Darikar Tijjaniya, Marigayi Shaikh Ibarhim Nyass dan kasar Senegal.
Ana yi wa Sayyada Maryam lakabi da Hadimar Alkur’ani wanda ta saudaukar da rayuwar kacokan wurin hidimar Alkur’ani Mai Girma.
Sayyada Maryam ita ce ta assasa cibiyar haddar Al’kur’ani ta Darul Kur’an a shekarar 1975.
A karkashin cibiyar, ta gina makaranta mai dalibai 1,600 a Dakar, babban birnin kasar Senegal.
Makarantar ta yaye dimbin mahaddata Alkur’ani daga kasar Senegal da makwabta irinsu Gambia da Guinea Bisau.
Marigayiyar ta kuma gina makarantar Majma’u Sheikh Ibrahim Nyass Alta’alimi a shekarar 1984 a Dakar.