Yadda ’yar shekara 11 ta rasu bayan malami ya yi mata fyade
Kotu ta tsare malamin da ya yi wa malamin ya yi wa ’yar shekara 11 fyade ta mutu a Kano.
Mahaifin wata yarinya ’yar shekara 11 da ta mutu bayan da wani malami ya yi mata fyade a Jihar Kano ya roki gwamnati da hukumomi kare hakkin dan Adam su kwato masa hakkin ’yarsa.
Mahaifin ya bayyana cewa ’yar tasa ta rasu ne sakamakon matsalar da ta samu a lokacin fyaden.
Malam Dauda Musa, da ke Karamar Hukumar Dalamya bayyana cewa bayan an yi wa ’yarsa fyade ne suka kai ta asibiti inda likitoci suka tabbatar da cewa ta samu munanan raunuka a al’aurarta sakamakon mummunan lamarin.
Ya ci gaba da cewa kusan watanni hudu yarinyar ba ta iya yin fitsari cikin sauki ba, don haka suka yawaita kai ta asibiti har a makon jiya da ta rasu.
- Majalisa ta gayyaci minista da NERC kan karin kudin lantarki
- Alkalin da ya dakatar da Ganduje ya janye umarnin
Don haka ya yi kira ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf; Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero; Kungiyoyin kare hakkin dan Adam da duk wanda abin ya shafa da taimaka musu wajen ganin an kwato hakkin marigayiyar.
Aminiya ta samu labarin cewa an kama wanda ake zargin, wanda malami ne a unguwar Dandinshe Quarters da ke karamar hukumar Dala.
Daga bisani an gurfanar da shi a gaban kotu mai lamba 47 da ke yankin Nomans Land, Kano, imda alkali ya da umarnin a ci gaba da tsare shi tare da dage shari’ar zuwa ranar 29 ga watan Afrilun nan da muke ciki.