’Yar shekara 12 ta kafa tarihin yin iyo a teku na kilomita 36

Hukumomi a kasar Indiya sun ce wata yarinya mai kimanin shekaru 12 ’yar asalin kasar ta kafa tarihin yin iyo a Tekun Maliya na tsawon kilomita 36.

’Yar shekara 12 ta kafa tarihin yin iyo a teku na kilomita 36

Hukumomi a kasar Indiya sun ce wata yarinya mai kimanin shekaru 12 ’yar asalin kasar ta kafa tarihin yin iyo a Tekun Maliya na tsawon kilomita 36.

Wata sanarwa da Ma’aikatar Tsaron kasar ta fitar a ranar Alhamis ta ce, “Jiya Rai, wacce ’ya ce ga sojan ruwan kasar, Madan Rai ta kafa tarihi ne bayan ta yi iyo tun daga mahadar Bandra har zuwa Kogin Worli na kasar Indiya.

“Nisan tafiyar da ta yi ya kai kimanin kilomita 36 a cikin sa’o’i takwas da mintuna 40 a ranar 17 ga watan Fabrairun 2021 da misalin karfe 3:45 na safe.

“Ta yi hakan ne duk da tana fama da wata cuta da take hanata cudanya ko yin magana da mutane, kuma ta yanke shawarar rungumar iyon ne saboda ta jawo hankulan mutane a kan masu fama da cutar,” inji sanarwar.

Rahotanni sun ce Kungiyar Masu Iyo ta Jihar Maharashtra ce ta sa ido a bikin kurmen.

Ko a bara dai sai da Jiya Rai dai ta yi iyo tun daga tsibirin Elephant zuwa yankin Gateway, mai nisan kimanin kilomita 14 a sa’o’i uku da mintuna 27.

Ma’aikatar Tsaron dai ta Indiya ta ce hakan ya sa ta zama yarinya mafi karancin shekaru mai fama da irin wannan cutar da ta yi tafiya mai nisa kamar haka a ruwa a duniya.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya