‘Yar shekara 12 ta kashe saurayinta da soya zuciyarsa
Jami’an tsaro sun kama wata yarinya ’yar shekara 12 mai suna Baleria inda ake tuhumarta da amfani da makami wajen kashe wani saurayinta da ke makwabtaka da ita mai suna Aledander Popobich a kasar Rasha tare da yanka wani sassan jikinsa. Rahoto ya bayyana cewa, Baleria bayan ta kashe Aledander Popobich ta soya zuciyarsa ta […]
Jami’an tsaro sun kama wata yarinya ’yar shekara 12 mai suna Baleria inda ake tuhumarta da amfani da makami wajen kashe wani saurayinta da ke makwabtaka da ita mai suna Aledander Popobich a kasar Rasha tare da yanka wani sassan jikinsa.
Rahoto ya bayyana cewa, Baleria bayan ta kashe Aledander Popobich ta soya zuciyarsa ta kuma ci inda ta bayyana zuciyar wanda ta kashe da ta yi mata dadi kamar yadda majiyar ta sanar. Wani jami’in ’yan sandan Rasha ya ce, Baleria ta daba wa Aledander mai shekara 21 wuka ne, kuma bayan mutuwarsa ta fara gunduwa-gunduwa da sassan jikinsa.
An dai tsare yarinyar tare da wani saurayinta mai suna Zbereb bisa zargin kisan Popobich sanadiyyar alakar soyayyar da ke tsakaninsu, wanda aka kwatanta da soyayya da karamar yarinya.
Binciken da hukumomin suka yi na nuna cewa, Baleria ta farke wa Popobich cikinsa ne don ganin abin da ke cikinsa. Yayin da jami’an ’yan sandan suka sanar da cewa, yarinyar bayan kashe Popobich ta hanyar daba masa wuka ta cire zuciyarsa da wani bangare na kirjinsa daga nan ta soya kuma ta cinye. ’Yan sanda sun kara da cewa, Baleria ta yi amfani da gatari waje cire masa hannu tare da daddatsa shi. Zbereb tare da yarinyar sun yi yunkurin tserewa amma ’yan sanda suka zagaye gidan suka kama su.
Makwabtan gidan ne suka sanar da jami’an tsaro lokacin da suka ji kuwwa a gidan. Sai dai shekarun yarinyar ba su kai a yanke mata hukunci ba, kamar yadda doka ta tanada.
Daya daga cikin jami’an tsaron da ya shiga gidan da aka yi kisan ya ce, alamun naman da aka toya bai yi kama da wanda suke gani a kasuwa ba.