’Yar shekara 12 ta zama uwa mafi karancin shekaru a Birtaniya

Wani uba a kasar Birtaniya ya bayyana alfaharinsa yayin da ’yarsa mai shekara 12 ta haihu da saurayinta, dan shekara 13, al’amarin da ya mayar da su iyaye mafi karancin shekaru a kasar.Yarinyar, wadda ba a bayyana sunanta ba, ta haihu a karshen makon da ya wuce daidai lokacin da take aji na bakwai, shi […]

’Yar shekara 12 ta zama uwa mafi karancin shekaru a Birtaniya

Wani uba a kasar Birtaniya ya bayyana alfaharinsa yayin da ’yarsa mai shekara 12 ta haihu da saurayinta, dan shekara 13, al’amarin da ya mayar da su iyaye mafi karancin shekaru a kasar.
Yarinyar, wadda ba a bayyana sunanta ba, ta haihu a karshen makon da ya wuce daidai lokacin da take aji na bakwai, shi kuwa saurayinta dan aji tara ne a wata makarantar. Mahaifin yarinyar ya bayyana goyon bayansa ga ’yarsa, amma ya ce ya girgiza a daidai lokacin da ya rage makonni hudu ta haihu, don a lokacin ya gano cewa babbar ’yarsa na dauke da juna biyu.
Mutumin da ya ce shi ne mahaifin yarinyar da ta haihu, ya kira gidan rediyon LBC, inda ya sauya sunansa da Greg, sannan ya bayyana wa mai gabatar da shirye-shirye Nick Ferari labarinsa. A cikin shirin rediyon ya bayyana cewa zai dauki nauyin kula da jaririn. Ya kuma yaba wa saurayin ’yar tasa, har ma ya yi masa jinjina.
Tuni dai uwar jaririn ta yi rajistar jaririnta a ofishin rajistar haihuwa, inda mahaifiyarta da wata mata suka yi mata rakiya. Kakar yarinyar, mai shekara 56, ta yi matukar girgiza jin cewa ta samu tattaba-kunne.
Jaridar Dailymail ta Birtaniya ta fitar da sunayen wadanda suke kananan iyaye, tun kafin su cika shekara 18 a duniya, al’amarin da ta ce har yanzu ba su da yawa a kasar, bisa la’akari da alkaluman kididdigar shekarun 1960 zuwa yau. Sannan jaridar ta yi tsokaci kan yadda gwamnati ke daukar nauyin irin wadannan kananan iyaye da abin da suka haifa. Amma idan kananan iyayen na iya daukar dawainiyarsu, ganin damarsu su ce.