’Yar shekara 18 ta banka wa saurayinta wuta a Binuwai

Wata budurwa ’yar shekara 18 mai suna Esther Alex, ta cinna wa saurayinta wuta a kan titin ZakiBiam da ke Unguwar Wadata a Makurdi, babban birnin Jihar Benuwai. Jami’ar Hulda da Al’umma ta rundunar ’yan sandan Benuwai, DSP Catherine Anene ta tabbatar da faruwar lamarin, wanda a cewarta budurwar ta yi amfani da man fetur […]

’Yar shekara 18 ta banka wa saurayinta wuta a Binuwai

Wuta
Hoto Daga Premium Times

Wata budurwa ’yar shekara 18 mai suna Esther Alex, ta cinna wa saurayinta wuta a kan titin ZakiBiam da ke Unguwar Wadata a Makurdi, babban birnin Jihar Benuwai.

Jami’ar Hulda da Al’umma ta rundunar ’yan sandan Benuwai, DSP Catherine Anene ta tabbatar da faruwar lamarin, wanda a cewarta budurwar ta yi amfani da man fetur ne wajen cinna wuta a dakin da saurayin nata ke ciki.

Anene ta ce a halin yanzu Esther Alex ta shiga hannu kuma za a ci gaba da gudanar da bincike domin gano dalilin wannan danyen hukunci da ta aikata.

“Ba mu da masaniya a kan dalilinta na aikata hakan, amma za mu yi mata tambayoyi kuma ina da tabbacin ta shiga hannu don yanzu haka an kawo mana ita.”

Aminiya ta samu cewa, Esther ta yi wannan aika-aika ne da misalin karfe 2.00 na daren ranar Litinin.

Kazalika, rahoton ya nuna cewa makwabta ne suka ankara da lamarin da ke faruwa yayin da suka jiyo sautin kururuwar matashin mai suna Chidinma Omah yana neman a kawo masa dauki.

Makwabtan sun kai wa matashin dauki wanda kusan duk jikinsa da konuwa inda suka garzaya da shi Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke birnin Makurdi.

Aminiya ta ruwaito cewa, wannan shi ne karo na hudu cikin watanni uku na makamancin faruwar wannan lamari na wani ya bankawa kansa ko masoyinsa wuta a Jihar.

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro

Lakurawa sun kashe ma’aikatan Airtel 3 a Kebbi