’Yar shekara 19 ta koma kamar ’yar shekara biyu

Wata yarinya ’yar shekara 19, mai suna Ajifa Khatun, wadda tsawonta bai wuce sentimita 78, kuma nauyinta bai wuce kilo 10 ba, ta koma tamkar ’yar shekara biyu a duniya. Iyayen wannan yarinya sun yi ta fafutikar neman magani ko wani sanadin da za ta zama budurwa daidai da shekarunta, amma abin ya ci tura.Mahaifiyar […]

’Yar shekara 19 ta koma kamar ’yar shekara biyu
’Yar shekara 19 ta koma kamar ’yar shekara biyu

 Ajifa tare da kannentaGa Ajifa nan tana dan tattakawaAjifa (ta biyu daga hagu) tana wasa da kananan yaraWata yarinya ’yar shekara 19, mai suna Ajifa Khatun, wadda tsawonta bai wuce sentimita 78, kuma nauyinta bai wuce kilo 10 ba, ta koma tamkar ’yar shekara biyu a duniya. Iyayen wannan yarinya sun yi ta fafutikar neman magani ko wani sanadin da za ta zama budurwa daidai da shekarunta, amma abin ya ci tura.
Mahaifiyar Ajifa, mai suna Apila Khatun, wadda ke zaune a kauyen Mirapur da ke gabashin kasar Indiya a Jihar Yammacin Bengal, ta ce, “Ajifa na son zuwa makaranta tare da ’yan uwanta. Kuma malamai na sha’awar yi mata wasa, don suna kaunarta”.
Da a ce shekarunta daidai suke da na kananan yara, ta fi sha’awar ta shiga cikin ’yan makarantar raino, amma kasancewar shekarunta 19, babu yadda za a yi. Wannan dai wata cuta ce da masana kimiyya ke yi wa lakabi da “Laron Syndrome”, wadda ta kama ta, al’amarin da ke nuni da cewa ta gama girma a daidai lokacin da ta cika shekara biyu a duniya, kuma a haka za ta zauna da jikinta a tsawon rayuwarta.
“Abin sha’awa ne ganin yadda Ajifa ke wutsul-wutsul a cikin gida,” a cewara mahaifiyarta, “Amma al’amarin na da ban takaici ganinta a wannan halin, musamman da ake da masaniyar cewa ba za ta kara girma ba”. Ajifa ba ta iya yin wata tafiya mai nisa, tamkar dai jaririya ’yar shekara biyu, don sai an dauke ta.
A halin yanzu, kanwarta ’yar shekara 17, Rini ke kai ta makaranta. Kuma suturar da ake sanya mata, dan kamfai ne da ’yar karamar riga ta jarirai. A wasu lokutan, sai a ga tana kada kai tamkar yadda kananan yara ke wasanni, sannan ta daga wa mahaifiyarta hannu idan za a tafi da ita zuwa makaranta.
Tamkar sauran iyaye, Apila, mai shekara 42 da mahaifin Ajifa, mai shekara 54, wanda ke aikin saka bututun ruwan famfo, suna matukar son ganin babbar ’yarsu ta girma, har ta yi aure.
Apila ta haifi ’ya’ya biyu, Rabiya da Rini, wadanda duk sun kere Ajifa a tsawo da girman jiki. Bayan shekara 14, sai likitoci suka bayyana mana cewa ta kamu da cutar daji ne, amma har yanzu ba mu samu likitan da zai iya warkar da ita ba. Mujallar Friday da ake wallafawa a Hadaddiyar Daular Larabawa ta ruwaito cikakken labarin.