’Yar shekara 2 ta rayu bayan ta kwana 6 a rijiya
Wani abin al’ajabi ya faru a garin Kwanar Farakwai da ke yankin karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna lokacin da aka gano wata yarinya mai suna Fauziyya, ’yar kimanin shekara biyu a cikin wata tsohuwar rijiya, bayan kwana biyar da bacewarta. Malam Musa Abdulrahman shi ne mahaifin Fauziyya, Aminiya ta zanta da shi a gidansa […]
Wani abin al’ajabi ya faru a garin Kwanar Farakwai da ke yankin karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna lokacin da aka gano wata yarinya mai suna Fauziyya, ’yar kimanin shekara biyu a cikin wata tsohuwar rijiya, bayan kwana biyar da bacewarta.
Malam Musa Abdulrahman shi ne mahaifin Fauziyya, Aminiya ta zanta da shi a gidansa da ke unguwar Alu domin sanin yadda wannan lamarin mai ban mamaki ya faru da diyarsa, inda ya bayyana cewa: “Ranar Laraba, 4 ga wannan watan da misalin karfe 9:30 na safe, matata Sa’adatu kuma mahaifiyar Fauziyya, ta tafi da ita gidan surukina, wanda babu nisa daga gidana, domin yin ta’aziyyar wata rasuwa da aka yi. A fahimtarmu bayan isarsu gidan ne Fauziyya ta fita waje kuma daga nan ne ta yi batar-dabo. Amma kimanin karfe 11:00 na safe ne mahaifiyarta da sauran jama’a suka fahimci cewa ba ta nan. Ba tare da wani bata lokaci ba, suka bazama neman ta, inda suka kewaye unguwar nan baki daya suna cigiya da kuma tambayar inda take, amma haka suka gama yawonsu ba tare da samun ta ko labarinta ba.
“Da misalin karke 1:30 na rana, ina zaune a gida, Sa’adatu ta aiko wani yaro, wanda shi ne ya shaida min abun da ke faruwa. Ba tare da wani bata lokaci ba, na isa gidan da suke. Ko da isa ta, ban yi kasa a gwiwa ba na wuce nemanta zuwa duk wani waje da nake tunanin zan same ta. Na yi ta kewaye-kewayena ba tare da haduwa da ko da mutum guda da ya ganta ko ya ji labarinta ba. Daga nan tare da sauran jama’a muka kara komawa gidan mai unguwa da fatan za mu same ta ko wani labari mai nasaba da inda take. Amma haka muka dawo babu kowanne. Haka dai muka ci gaba da nemanta tare da taimakon ’yan uwa da abokan arziki ba tare da samun nasara ba, har dare ya yi sosai. Da gari ya waye, muka ci gaba daga inda muka tsaya, inda muka bi dukkannin rijiyoyin unguwar nan muna duba su a tunanin ko wata kila ta fada ciki, ba a sani ba. Amma haka muka gama bin su, daya bayan daya, ba tare da samun ta ba. Haka dai labarin ya ci gaba da kasancewa har tsawon kwana biyar bayan batanta.
“A cikin wadannan kwanakin ba na iya ko runtsawa, haka nake ganin dare da rana. Yanayin ba mai dadi ba ne, amma a hakan nake tausar kaina da kuma mahaifiyar Fauziyya, wadda tun bayan faruwar lamarin, ba ta iya ko magana, sai kuka. Yanayin da ta shiga ba ya rasa nasaba da yadda ta kasance ita ce diyarta ta fari. A rana ta uku ne kuma ni kaina na barke da gudawa, wadda ba ta tsaya ba, har sai bayan bayyanarta. A gaskiya damuwata ta tsananta a cikin wannan ranar, saboda a kullum garin Allah ya waye, gani nake kamar rana ba za ta fadi ba, ba tare da mun gano ta ba. Musamman ta la’akari da ganin yadda nake bai wa malamai kudi don su taya ni rokon Allah da addu’o’in da za su bayyana ta. Hakazalika, a wani yunkurin ganin an gano ta, na ba sankiran garin nan lada domin ya bi gida-gida da kuma unguwa-unguwa ya yi shelar cigiyarta, amma haka ya kammala aikinsa, ba tare da hakarmu ta cimma ruwa ba. Wannan ya sa muka fara tunanin daukar dangana, inda muka fara addu’o’in Allah Ya bayyana mana ko da gawarta ce”.
Ya ci gaba da cewa,“A rana ta biyar kuma cikin yini na shida, wato ranar Litinin 9 ga watan nan ne, bayan sallar Isha’i, wadansu mutane uku da ke zaune a gefan wani masallaci a kusa da wata tsohuwar rijiya da aka toshe saboda an daina amfani da ita, kimanin shekara 20 da suka wuce, suka fara jin kuka daga cikin rijiyar. Kodayake da farko wasu daga cikinsu sun zaci ko kukan mage ne, amma sai mutum guda a ciki ya ce: ‘Mage, ko dai diyar Musa? ’ Tana ci gaba da tsandara kuka ne, sai wani kuma ya ce, ‘ita ce Wallahi’. Ba su bata lokaci wajen gane ta ba, saboda yadda batanta ya zama wani labari da kowa ya sani a garin nan.
“A ciki su ne wani ya kira ni ta waya ya sanar da ni cewa, ‘an ganta a cikin rijiya’. Da fari ni kaina ban fahimci cewa an same ta ne a raye ba. Ni ina zaton fara jin warin gawarta ne daga rijiyar ya sa aka fahimci cewa a ciki ta mutu. Saboda haka abokaina da muke tare da su a lokacin har sun fara min ta’aziyya tare da tambaya ta cewa da daren za a kai ta (jana’iza) ko sai gobe da safe. Daga nan na nufi rijiyar inda kuma na tarar da kusan dukkannin jama’ar garin nan, ana shewa da kururuwar neman gudummuwar wanda zai shiga rijiyar don ya fito da ita. A lokacin ne na fahimci cewa ashe ba ta mutu ba, kuma nan take na yi hamdala ga Ubangiji.”
Malam Habibu Musa, shi ne kanen mahaifiyarta kuma mutumin da ya ciro Fauziyya daga rijiyar, a zantawarsa da Aminiya ya ce: “Gidana kusa yake da rijiyar kuma hayaniyar jama’a ce ta sa na fito waje don na binciki abun da ke faruwa. Ko da isata wajen ban yi wata-wata ba na shiga rijiyar, daga bisani kuma aka miko min fitila da maburgi da kuma fatanya. Na tone ta har sai da ya kai zurfin kusan gaba 10 kafin na samo yarinyar a cikin wani kogo babba da ya kai girman daki, a kwance tana tsotson yatsa kamar yadda ta saba. Aikin ceton ya kwashe ni kimanin minti 30 kafin na kammala.”
Wani abun da yake kara daure wa jama’a kai shi ne yadda saman rijiyar ta kasance toshe da gungumen itatuwa da kayoyi, kuma mutane sun zaci zurfinta bai fi a ce gaba guda ba. Har ila yau, saboda rijiyar kusa take da Gidan Magajin Aska, wato gidan da su Fauziyya suka je ta’aziyya, a lokuta da dama bayan bacewarta, an sha zuwa bakin rijiyar da tunanin ko nan ne ta fada, amma sai a ga babu wata alamar da ke nuni da cewa tana ciki.
Da wakilinmu ya tambayi mahaifinta yadda ya ganta a lokacin da aka fito da ita, sai ya ce: “Gaskiya a lokacin duk wanda ya dube ta ba zai so ya kara ba, saboda yadda ta galabaita. Sai ka ce ta yi fama da ciwon amai-da-gudawa ne saboda tsananin rama da firgici da take ciki. Amma kuma babu wata alamar jin ciwo ko wani tabo a jikinta.
“Daga nan muka ba ta madara ta karba ta sha. Bayan ta gama sha, sai na kira wani ma’akacin lafiya mai suna Gambo Sa’idu, wanda ke aiki a wani asibiti da ke garin Zangon Aya, ya zo gidana, inda ya ba ta karin ruwa har na tsawon kwana biyu daga nan ne kuma sai jikinta ya ci gaba murmurewa har zuwa yanzu da ta dawo hayyacinta sosai, kusan kamar yadda take kafin fadawarta rijiyar. Daga faruwar wannan lamarin na samu kiran waya daga wurare da dama, ana jajanta min da kuma taya ni murnar bayyanata da Allah Ya yi. Da wannan nake godiya ga Allah da kuma dukkannin jama’a na nesa da na kusa da suka taimaka min a lokacin faruwar wannan abun al’ajabin.” Inji shi.
A zantawarmu da Malam Gambo Sa’idu, wanda shi ne Malamin lafiya da ya duba ta bayan an ceto ta daga rijiyar, ya ce: “Wannan abu ne da ban taba gani ko ji ba a tsawon tarihin aikina. Amma cikin yardar Allah ga shi bayan kara mata ruwa da ba ta wadansu magunguna da na yi, ta samu sauki cikin ’yan kwanaki. Ya zama wajibi mu gode wa Ubangiji. Saboda yunwa kadai da ta yi ajalinta a tsawon kwanakin da ta yi a cikin rijiyar. Har ila yau, da a ce akwai maciji a rijiyar, ko a ce ta ji rauni lokacin da ta fada ciki, wadannan ma za su iya yi mata illar da ka iya yin sanadiyyar rasuwarta a cikin rijiyar.” Inji shi.