’Yar shekara 23 da ta auri tsoho mai shekara 80

Wasu da dama sun zargi Xiaofang da auren Mista Li don neman kuɗi.

’Yar shekara 23 da ta auri tsoho mai shekara 80

Labarin soyayyar da ba a saba gani ba tsakanin wata budurwa mai suna Xiaofang ’yar shekara 23 a lardin Hebei na ƙasar China da wani tsoho mai shekara 80 da ya haɗu da ita a gidan kula da tsofaffi ya haifar da zazzafar muhawara a ƙasar.

Xiaofang mai shekara 23, ta gamu da ‘masoyinta’ ne a lokacin da take aikin sa-kai a wani gidan ajiye tsofaffin da suka yi ritayar aiki a Lardin Hebei.

Mista Li mai shekara 80 mazaunin wurin ne kuma su biyun nan da nan suka zama abokai bayan sun fahimci cewa suna son juna da abin da suke so iri ɗaya.

Amma, bayan wani lokaci, abokantakarsu sai ta riƙa ƙaruwa, saboda dattako da natsuwa da hikimar Mista Li waɗanda suka jawo hankalin Xiaofang, yayin da shi kuma himma da kirkin Xiaofang suka jawo hankalinsa.

Abin takaici, dangin budurwar ba su yarda da alaƙarta da mutumin da ya kai kakanta ba, amma ta yanke shawarar bin abin da zuciyarta ke so kuma ta yanke alaƙa da iyayenta don kasancewa da Mista Li.

Labarin Xiaofang da Li ya haifar da zazzafar muhawara a kafafen sadarwar Intanet, inda mutane da yawa daga cikin masu amfani da shafukan ke cewa, sun kasa fahimtar amincewar da budurwar ta yi da alaƙarta da tsohon, wasu kuma suka yaba mata kan jajircewa da sadaukar da kai ga Mista Li.

A cewar shafin Intanet na China mai suna Sohu, ma’auratan da ba a saba gani ba kwanan nan sun yi aure a cikin sauƙi amma mai ƙayatarwa.

Duk da cewa babu ɗaya daga cikin iyalansu da ya halarci bikin, su biyun sun yi musanyar alwashi, inda suka yi alƙawarin kasancewa tare da juna cikin ƙoshin lafiya ko rashin lafiya.

Wasu da dama sun zargi Xiaofang da auren Mista Li don neman kuɗi. Duk da cewa ita ce mai ciyar da su abinci.

Saboda yawan shekarunsa da rashin cikakkiyar lafiyarsa, Mista Li zai iya dogara ne kawai ga kuɗin fanshonsa, don haka ya rage ga Xiaofang ta kula da mafi yawan matsalolin kuɗinta.

Duk da haka, ta yi maraba da ƙalubalen da za ta fuskanta, tana mai cewa komai yana yiwuwa tare da Li idan suna tare.

Xiaofang tana yawan wallafa saƙon hotuna da bidiyonta ita da Mista Li a shafukan sada zumunta, waɗanda mutane da yawa ke fassarawa a matsayin hujjar soyayya ta gaskiya.

Sai dai sukar da take sha kan bambancin shekarunsu da ce-ce-ku-ce na haifar da zargin da ake yi wa budurwar mai shekara 23 cewa tana cikin wannan dangantakar ce kawai don kulawa da kuma ra’ayi.

Al’ummar ƙasar China dai na bayyana ra’ayinsu kan dangantakar Xiaofang da Mista Li, inda wasu suka bayyana shi a matsayin labarin soyayya da ya wuce shekaru, wasu kuma na iƙirarin tazarar shekarun ya yi yawa, kuma soyayyarsu ba za ta iya zama ingantacciya ba.

Duk da muhawarar, masoyan biyu sun ci gaba da gudanar da rayuwarsu, suna bayyana soyayyar juna da kuma yin alƙawarin zama tare muddin suna raye.

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu