‘Yar shekara 68 ta haihu bayan ta shekara 52 da aure babu haihuwa
Wani abin mamaki ya faru a garin Ibadan babban birnin Jihar Oyo, inda tsohuwar mata mai kimanin shekara 68 a duniya ta haifi da namiji a wani asibiti a Ibadan bayan ta shekara 52 da yin aure babu haihuwa. Wannan mata ‘yar asalin garin Ibadan ta haihu a wani asibiti a makon day a gabata, […]
Wani abin mamaki ya faru a garin Ibadan babban birnin Jihar Oyo, inda tsohuwar mata mai kimanin shekara 68 a duniya ta haifi da namiji a wani asibiti a Ibadan bayan ta shekara 52 da yin aure babu haihuwa.
Wannan mata ‘yar asalin garin Ibadan ta haihu a wani asibiti a makon day a gabata, kuma wannan ne karo na biyu da ta dauki ciki a tsawon rayuwarta, amma kuma wannan danta na farko duk kuwa da shekarunta.
Da take magana da manema labarai a gadon asibiti a Yemetu da ke Ibadan, ‘yar kasuwar ta ce ta taba daukan ciki wanda shi ne na farko a 2 ga watan Janairu na shekarar 1966, sannan tun lokacin da wancan cikin ya zube, ta yi duk mai yiwuwa wajen ta sake daukan wani cikin amma abin ya ci tura, sai kuma yanzu da Allah Ya nufa sai gashi ba ma daukan cikin ba, har ta sauka lafiya.
Ta ce a kokarinta na samun haihuwa, an mata tiyata sau biyu, sannan kuma ta je wajen masu addu’o’i da yawa da nufin ko Allah zai taimaketa ta samu haihuwa, sai kuma yanzu gashi ta samu, wanda hakan ya sa take godiya ga Allah bisa wannan kyauta da ya mata.
Ta ce wannan dan kyutar Allah ce kawai, domin ta fara ganin canji ne a al’adarta tun kimanin shekara 10 da suka gabata amma babu ciki, sai a bara ne kawai ba zato ba tsammani sai gashi ta dauk ciki, sai kuma yanzu ta haihu.
Matar wadda ta ki amincewa ta bayyana cikakken asalinta da kuma mijinta da kuma yadda likitoci suka taimaka mata har ta haihu, ta ce tana bukatar hutu ne yanzu domin a cewarta likitoci sun ce za ta zauna a asibiti na sama da wata daya kafin ta haihu, kuma hakan aka yi.
“Ban samu wata matsala ba da farko a lokacin da na dauki cikin a bara, amma mako daya kafin na haihu, sai tafiya ya zama yana min wahala saboda gajiya. Ina matukar godiya da likitocin da suka taimaka min har na sauka lafiya,” inji ta.