’Yar shekara 8 ta kamu da zazzabin Lassa a Gombe
An samu bullar zazzabin cutar Lassa a Jihar Gombe inda likitoci suka tabbatar da cewa wata yarinya ’yar shekara takwas daga kauyen Lamban a karamar Hukumar Yamaltu Deba ta kamu da zazzabin Lassa.Wani babban likita a Asibitin kwararru na Gombe, kuma Daraktan Kula da Sha’anin Lafiya a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Dokta Joshu’a Abubakar, ya […]
An samu bullar zazzabin cutar Lassa a Jihar Gombe inda likitoci suka tabbatar da cewa wata yarinya ’yar shekara takwas daga kauyen Lamban a karamar Hukumar Yamaltu Deba ta kamu da zazzabin Lassa.
Wani babban likita a Asibitin kwararru na Gombe, kuma Daraktan Kula da Sha’anin Lafiya a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Dokta Joshu’a Abubakar, ya tabbatar wa manema labarai haka a Gombe.
Ya ce an tabbatar yarinyar ta kamu da zazzabin Lassa ne ta hanyar daukar jininta a tura Legas don yin gwaji bayan da ta kamu da zazzabi mai zafi.
A cewarsa yanzu haka an killace ta a wani daki a Asibitin kwararru na Jihar ana kula da ita, kuma ya ce an kawo ta ne daga wani asibiti mai zaman kansa.
Dokta Joshu’a, ya ce yanzu tawagar kwararrun likitoci a jihar suna aiki don gano hanyar da yarinyar ta kamu da wannan zazzabi don ba da kariya ga iyaye da sauran ’yan uwanta.
Ya ce an samu rahoton cewa zazzabin Lassa ya shafi mutum bakwai a jihar amma bincike ya tabbatar da cewa biyar daga cikinsu ba su dauke da zazzabin, yarinyar ce kawai aka tabbatar ta kamu, yayin da wani mutum daya ana kokarin tantacewa ko shi ma yana dauke da cutar.
Dokta Joshu’a, ya yi kira ga jama’a su kasance masu kula da tsabtar muhallansu da kuma kansu sannan su kawar da berayen da ke gidajensu.
“Kada ku rika barin abincinku a bude saboda gudun kada beraye su sa baki ko su yi fitsari a ciki,”inji Dokta Joshu’a.
Sai ya shawarci jama’a su hanzarta kai rahoton bullar duk wata cuta da suka gani ba su gane kanta ba ga hukumomin lafiya don yin gwaji.