’Yar shekara 85 ta yi wuf da dan shekara 25
Kafin faranta wa wadansu rai, da farko ka faranta wa kanka rai.
Wani matashi mai suna Muima mai shekara 25 ya girgiza mutane da yawa bayan ya bayyana niyyarsa ta auren wata tsohuwa mai suna Thereza mai shekara 85.
Saurayin ya fada cikin kogin soyayya da tsohuwar ce inda yanzu haka suke shirin a daura masu aure nan ba da jimawa ba a hukumance.
- Azumin Sitta Shawwal a Musulunci
- Saudiyya ta kama wasu ’yan Najeriya da suka daga hotunan ’yan siyasa a Harami
Dukkansu sun kudirta za su zauna da juna tsawon rayuwarsu duk da hakan bai dace da ra’ayin wadansu mutane masu yawa ba. “Wannan shi ne zabina,” inji saurayin mai shirin zama ango.
“Wannan shi ne farin cikina, kamar yadda kowa yake da nasa.
“Kafin faranta wa wadansu rai, da farko ka faranta wa kanka rai kuma ka yanke shawara ba bisa ra’ayin wani ba,” kamar yadda saurayin ya shaida wa tashar YouTube ta Afrimad English.
Muima da abokansa sukan shiga gidan tsohuwar bayan sun dawo farauta a gidan da Thereza take zaune a matsayin haya.
Ita dai Thereza takan kira Muima da mijinta, wanda a farko ya dauka da wasa ne, amma zuwa wani lokaci, sai suka fara soyayya.
“Yadda take kula da ni ya sa nake sonta kuma kodayake ita tsohuwa ce a gaskiya, za ta iya zama kakata, amma ina sonta a haka,” inji Muima.
Ya ba da labarin cewa wata rana abokin aikinsa ba ya nan, yana jin yunwa kuma ba ya da abinci a gidansa.
Sai tsohuwar ta kawo masa abinci ta yi masa hidima da kula sosai kafin ta nemi ya sumba ce ta, wanda ta wajabta masa yi. Yayin da huldarsu ta yi karfi.
Ya ce shi da ita suna shafe lokaci suna wasa, suna daga juna kuma suna yin tafiye-tafiye duk da yawan shekarun Thereza.
Mafi yawan mutane wadanda ba su san labarin soyayyarsu ba, suna tunanin wasan kaka ne da jika suke yi.
Thereza tana da jikoki da suka girmi saurayin nata, amma ba ta jin kunyar zama da Muima.
“Ina da ’ya’ya takwas da jikoki 20.
“Dangane da shekarun saurayina, zai iya zama jikana na biyar. Yana so na kuma ina son sa. A shirye nake in saka rigar aure da zoben aurena da shi,” inji ta.
Muima ya ce shi ma a shirye yake ya biya sadakin amaryar tasa, kamar yadda aka umarce shi ya biya da shanu 12 wadanda ’ya’yan Thereza suka nema.