’Yar shekara 90 ta shiga makarantar tattaba-kunnenta

Wata tsohuwa ’yar shekara 90 ta shiga makarantar da tattaba kunnenta shida ke zuwa, don haka ake ganin ita ce daliba mafi tsufa a duniya, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta ruwaito. Wannan tsohuwa mai suna Priscilla Sitienei tana sanya kayan makaranta irin na tattabakunnenta, a lokacin da take rubuta sunayen dabbobi a […]

’Yar shekara 90 ta shiga makarantar tattaba-kunnenta
’Yar shekara 90 ta shiga makarantar tattaba-kunnenta

Wata tsohuwa ’yar shekara 90 ta shiga makarantar da tattaba kunnenta shida ke zuwa, don haka ake ganin ita ce daliba mafi tsufa a duniya, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta ruwaito.

Wannan tsohuwa mai suna Priscilla Sitienei tana sanya kayan makaranta irin na tattabakunnenta, a lokacin da take rubuta sunayen dabbobi a cikin harshen Ingilishi.
A halin yanzu tana halartar makarantar share fagen karatu ta Leaders bision Preparatory na tsawon shekara biyar, sannan ta shafe shekara 65 tana aikin unguwar zoma a kauyensu na Ndalat da ke tsaunukan gabar ruwa. A hakikanin gaskiya ma ita ta karbi haihuwar wasu daga ’yan ajinsu, wadanda shekarunsu suka kama daga 10 zuwa 12.
Wannan dattijuwa ana yi mata lakabi da “Gogo” ma’ana, a harshenu na Kalenjin ana nugfin Kaka, ta ce a matsayinta na ’yar shekara 90, tana koyon rubutu da karatu ne, saboda a lokacin yarintarta ba ta samu damar yi ba.
Ta fi jin dadin yin magana da harshenta na Kalenjin fiye da Ingilishi, inda ta yi bayanin dalilin da ya sanya ta koma makaranta.
“Ina son karanta Baibul. Kuma ina son karfafa wa yara gwiwar neman ilimi. Domin akwai tofafffin yara da ba su samu shiga makaranta ba. Wasu ma har suna da ’ya’ya,” inji ta.
Gogo takan tunkari yara ta tambaye su, me ya sa ba ku zuw amakaranta? Amsar da suke ba ni ita ce: “Wai sun tsufa,” ita kuwa sai ta ce musu, “ni ma ina zuwa makaranta don haka ya kamata ku shiga.
A cewarta: “Ina ganin yaran da ba su da makoma, ’ya’yan da suka rasa iyayensu maza, suna ta kai kawo ba tare da wata makoma ba. Shi ya sa nike son karfafa musu gwiwa su shiga mkaranta.
Da farko wannan makaranta ba ta karbi Gogo ba, amma da aka fahimci cewa da gaske take sai aka kyaleta. Shugaban makarantar, Dabid Kinyanjui, yana da tabbacin cewa Gogo da ke kwana a makarantar kauyen, abin misali ce ga saurna ’yan ajinsu.