‘Yar shekara 91 ta shekara 71 tana aiki ta ce ba za ta daina ba

Tsohuwa mai shekara 91 Elena Griffing, wadda ta shafe shekara 71 tana aikin asibiti ta ce ba za ta ajiye aiki ba, har sai an sallameta ko ta shiga akwatin daukar gawa, kamar yadda shafukan sadarwar intanet da suka hada da yahoo da facebook suka baza labarinta. Kuma ta bayyana yadda take kasancewa cikin annashauwa, […]

‘Yar shekara 91 ta shekara 71 tana aiki ta ce ba za ta daina ba

Tsohuwa mai shekara 91 Elena Griffing, wadda ta shafe shekara 71 tana aikin asibiti ta ce ba za ta ajiye aiki ba, har sai an sallameta ko ta shiga akwatin daukar gawa, kamar yadda shafukan sadarwar intanet da suka hada da yahoo da facebook suka baza labarinta. Kuma ta bayyana yadda take kasancewa cikin annashauwa, domin ba ta lokacin damuwa ballanata ta shiga bakin ciki.

A wannan karni na 21 da ake karakainar sauya aiki don smaun ci gaba, mafi karancin lokacin da ake sarayarwa a kamfani shekaru biyu ne kawai. Su kuwa wadanda aka Haifa bayan yakin duniya na biyu da sauran al’ummmomin da suka biyo baya, wannan ba al’adarsu ba ce. Biyayya da jajircewa a kamfani guda ko samun kwarewa, har yanzu shi ke jan mutane da dama a ayyuklansu, kamar yadda shafin sadarwar AOL ya nuna a jerin makalolinsa kan jajircewa da biyayyar ma’aikata, wadanda suka dade a aikinsu tsawon shekaru. Ko za su yi murabus? Ko sun shirya?

“Ranar 10 ga Afirilun 1946, na kama iki, kuma har yanzu ban a jiran samun wwani aiki, tunda yanzu shekara 71 ke nan,” a cewar Elena Griffing wata jamiar hulda da majiyata a a Cibiyar kula da lafiya ta Sutter Health Alta Bates da ke Berkeley.

A halin yanzu shekarunta 91, matar da ke zaune a Orinda ta Califonia a Amurka ta ce kasancewarta ma’aikaciyar kula da lafiya lokacin da ta fara aiki tana da shekara 20, lamkarin ya kasance da “ban mamaki.”

Abokan aikinta sun siffatanta a amtsyain mai “jan hali” da ta “tsayu da kanta” bisa la’akari da wasu dalilai da suke ganin sun taimaka wajen kai-kawo da dakunan majiyata tana tafe da takalmanta masu tsini cike da annnashuwa wajen gudanar da aikinta a kowace rana.

Shugaban Cibiyar kula da lafiya ta Sutter Health Alta Bates Summit Medical Center ta yi wa Gritting lakabin “zuciya da ruhi” na asibitin, kuma irrin tasirinta a wajen aikin da al’adun bai yi kama da komai da ya wuce “ban mamaki.”

Griffing ta yi fama da cutar matsalar juya akalar kwararan isjkar odygen a cikin jinni, wadda ake kira da “hemoglobin disorder”lokacin tana da shekara 19, sai ta kwanta a asibitin da ya askance nan take aiki. Ta kwanta tsawon wata hudu, har ta warke. Wata rana, wasu masu aikin dakin gwaji suka yi korafin cewa sakatare bai zo aiki ba, kuma lamarin yana dakushe musu kwarin gwiwar aiki. Griffing ta ce daya daga cikinsu ya tuntubeta cewa ko ke sakatariya ce? Za ki samu aiki.”Lamarin dai ya zama tarihi.

Bayan ta fara aikin mai karbar baki, Griffing sai ta koma sashen gwajin cututtuka da bincike, inda ta rika rubuta rahotanni da sakamakon gwaje-gwaje tun kafin a fara amfani da kwamfuta a fannin. Daga nan sai Griffing ta ce “Komai da hannu ake yinsa.”

Yanzu Griffing jakadiyyar asibitin ce mai kimar mutuntaka, wadda ta tattara kauna da tausasa wa ga majiyata da ke kwwance a asibiti. Griffing kan kasance cike da murrmushi, inda takan kawo wa majiyatan da suka manta kayansu, saboda ta san muhimmancin fara’a a wajen sadarwa, tamkar zuba jari ne a mutanen da ka hadu da su a wajen aiki. Da irin wannan dabi’ar, ba zabin mamaki ba ne Griffing kwanaki hudu kacal na rashin lafiya ta taba dauka a shekarunta 71 tana aiki, kuma har yanzu ta har zuwa har ta ce zai yi wuya ta bari.

“Ba ni da lokacin dugunzuma cikin damuwa. Na ki yarda in shiga damuwa. Ba ni da lokacin bakin ciki, ina cike da dimbin farin cciki da annashuwa,” a cewar Griffing, lokacin da take tattaunawa kana bin da take ganin shi ne sirrin nasararta. “Kana aiki kowace rana. Sai mun yi tunani don warware matsalar kowace rana. Wannan ita ce hakkikanin gaskiyar lamari.”

Ko za ta ajiye aiki? Griffing ta ce za ta ci gaba nan da shekara guda, amma tana fatan ta samu damar yin aiki na a kalla sheekara hudu, har ta kai shekara 75.

A cikin fara’a ta furta cewa: “Zan ajiye aiki ne idan aka kore ni ko a ka saka ni a akwatin gawa (makara).