’Yar shekara daya ta sawo wa babanta mota ta cikin wayar salularsa

Wata yarinya ’yar shekara daya ta lallatsa wayar salular babanta har ta sayo mas amota a lokacin da take wasa da wayaer. Mahaifin yarinyar da ya fara cinikin motar, amma sai ya dakatar da cinikin, ita kuwa wannan’ya tasa tana zuwa sai ta karasa masa. Al’amarin dai ya auku ne a kasar Amurka. Paul Stoute […]

’Yar shekara daya ta sawo wa babanta mota ta cikin wayar salularsa
’Yar shekara daya ta sawo wa babanta mota ta cikin wayar salularsa

Wata yarinya ’yar shekara daya ta lallatsa wayar salular babanta har ta sayo mas amota a lokacin da take wasa da wayaer. Mahaifin yarinyar da ya fara cinikin motar, amma sai ya dakatar da cinikin, ita kuwa wannan’ya tasa tana zuwa sai ta karasa masa. Al’amarin dai ya auku ne a kasar Amurka.

Paul Stoute da ke zaune a Portland ta Jihar Oregon a kasar Amurka, ya ce ya samu sakon taya murnar sayen mota daga kamfanin hada-hadar kasuwanci ta shafukan kwamfuta na eBay, inda aka bayyana masa cewa ya sayi mota kirar Austin-Healey Spriet ta shekarar 1962, a kan kudi Dala 225.
Babban abin mamaki ga Stoute, shi ne shi dai bai yi wannan cinikin ba,kamar kafar yada labarai ta PTI ta ruwaito.
Iyayen yarinyar sun shirya karbar wannan kurkuren cinikin motar. Don haka Paul Stoute ya ce zai gyara motar, ya ajiyeta, harsai ’yarsa ta kai shekarta 16 ko ta kamala babbar makaranta sai ya mika mataamatsayin kyauta.