’Yar shekara hudu ta azumci Ramadana
Yarinya ’yar shekara hudu a birnin Jedda da ke kasar Saudiyya ta azumci kwana 29 na watan Ramadanan bana. A daidai lokacin da kananan yara irin Zainab Azhar Butt kesarayar da lokacinsu wajen wasanni, amma wannan yarinya ta zama abin koyi da doka misali ga al’umma.Mahaifin Zainab, Azhar Hanif Butt, wanda ya shafe shekaru yana […]
Yarinya ’yar shekara hudu a birnin Jedda da ke kasar Saudiyya ta azumci kwana 29 na watan Ramadanan bana. A daidai lokacin da kananan yara irin Zainab Azhar Butt kesarayar da lokacinsu wajen wasanni, amma wannan yarinya ta zama abin koyi da doka misali ga al’umma.
Mahaifin Zainab, Azhar Hanif Butt, wanda ya shafe shekaru yana aiki a birnin Jedda, kamar yadda ya bayyana wa jaridar Arabnews.
Ya ce duk da cewa a fannin kula da lafiya, likitoci ba za su amince ta yi azumi ba, babu wata alama ta gajiyawa da ’yarsa ta nuna a lokacin da take azumin Ramadana. Wannan ’yar shekara hudu ta zama abin alfaharin al’umma ganin ta shafe kwanaki 29 tana azumi.
“Mun kyaleta ta ci gaba, saboda irin zummar da take da ita, amma ba ni da tabbacin cewa za ta iya kai wa har karshe,” inji mahaifinta, Azhar Hanif but.
Ya ce ba na son karya kwarin gwiwarta na son yin azumi. Sai dai a kodayaushe muna lura da ita a lokacin da take azumin daukacin kwanakin ramadana.
Jaridar Arabnews, ta ruwaito cewa, sauran ’yan uwan Zainab, wadanda suka hada da ’yayyaenta maza da mata, suna cike da farin cikin wannan matsayi da ’yar uwarsu ta kai. A Musulunci dai ba a bukatar karamin yaro ya yi azumi, don ba farilla ba ce a kansa/kanta, har sai ya/ta balaga. Kuma a fannin likitanci ma ba a yarda kananan yara su yi azumi ba, don ba za su iya ba.