’Yar tsala

Kayan hadi: . Gero . Mangyada . Yis . Gishiri . Dakakken yaji mai kuli-kuli   Yadda ake yi: Za a surfa gero sannan a bushe a wanke sai a shanya, idan ya bushe sai a kai a niko a tankade shi, sai kuma a jika yis da ruwan zafi. Sai a dauki ruwan yis […]

’Yar tsala

Kayan hadi:

. Gero

. Mangyada

. Yis

. Gishiri

. Dakakken yaji mai kuli-kuli

 

Yadda ake yi:

Za a surfa gero sannan a bushe a wanke sai a shanya, idan ya bushe sai a kai a niko a tankade shi, sai kuma a jika yis da ruwan zafi. Sai a dauki ruwan yis din a kwaba garin geron da shi bayan an sanya masa gishiri. Idan an gama kwabawa sai a bar shi ya dade kamar misalin sa’a biyu zuwa uku, ya danganta da yanayin gari, ma’ana idan lokacin zafi ne ba sai ya dade sosai ba. Idan kullin ya kumbura ko ya tashi sai a dan kara ruwa a juya ana son kwabin ya zama da dan ruwa-ruwa. Idan aka gama hadawa sai a asa cokali a rika diba ana soyawa a cikin mangyada. Idan ’yar tsalar ta soyu sai a kwashe. Ana ci da yaji wanda ya ji kulikuli sosai.