Yara 19 sun mutu bayan kifewar kwale-kwale a Kwara
Rahotanni daga unguwar Lafiagi a karamar hukumar Edu ta jihar Kwara na cewa, kifewar kwalekwale ya yi sanadiyyar rasuwar yara 19 a kogin Neja ranar Asabar. Rahotan ya ce, yaran na kan hanyar su ne don halartar bikin aure a jihar Neja, kwalekwalen yana dauke da fasinjoji 22 yawancin su yara. Majiyarmu ta gano cewa […]
Rahotanni daga unguwar Lafiagi a karamar hukumar Edu ta jihar Kwara na cewa, kifewar kwalekwale ya yi sanadiyyar rasuwar yara 19 a kogin Neja ranar Asabar.
Rahotan ya ce, yaran na kan hanyar su ne don halartar bikin aure a jihar Neja, kwalekwalen yana dauke da fasinjoji 22 yawancin su yara.
Majiyarmu ta gano cewa yaran 19 sun rasu ne bayan kifewar kwalekwalen yayin da aka ceto biyu.