Yara 2m ke bukatar agajin jin kai a Nijar —UNICEF
Da farko UNICEF ya yi hasashen miliyan 1.5 ke fama da rashin abinci mai gina jiki, ciki har da akalla 430,000 da ke fama da tsananin cutar yunwa.
Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa kananan yara sama da miliyan biyu ne ke bukatar agajin jin kai a Jamhuriyar Nijar sakamkon rikicin masu ikirarin jihadi da kuma juyin mulkin baya-bayan a kasar.
Rahoton UNICEF kafin rikicin baya-bayan a Nijar ya kiyasta cewa yara ’yan kasa da shekaru 5 miliyan 1.5 ke fama da rashin abinci mai gina jiki, ciki har da akalla 430,000 da ke fama da tsananin cutar yunwa.
- Nijar ta samu tallafin tirela 300 na abinci daga Burkina Faso
- Nijar: ECOWAS ta yi watsi da gwamnatin rikon kwaryar shekara 3
Rahoton UNICEF ya nuna adadin na iya karuwa idan farashin abinci ya ci gaba da hauhawa, da kuma tabarbarewar tattalin arzikin iyalai, da na kudaden shiga.
Bugu da kari, karancin wutar lantarki da tuni ya yawaita a jamhuriyar Nijar da kuma karuwar takunkuman da kungiyar ECOWAS ta kakaba wa kasar, sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi, na iya yin illa ga tasirin alurar rigakafin jarirai da aka adana a cibiyoyin kiwon lafiya.