Yara 3 sun nutse a ruwa a ƙauyen Jigawa

Rahotanni sun nuna cewar yaran sun nutse ne yayin yin ciyawa a gefen tafkin.

Yara 3 sun nutse a ruwa a ƙauyen Jigawa

Garin Tulla da ke ƙaramar hukumar Buji a Jihar Jigawa, ya tashi da jimami bayan wasu yara mata guda uku sun nutse a ruwa.

Shaidun gani da ido sun ce Fatima Sule (mai shekara 12), Nasiya Sale (mai shekara 12) da Huwaila Sa’adu (mai shekara 13), sun nutse a ruwa yayin yankar ciyawa a kusa da wani tafki domin ciyar da dabbobinsu.

An yi ƙoƙarin ceto yaran, amma ba a yi nasara ba har rai ya yi halinsa.

Kakakin Hukumar Sibil Difens na Jihar Jigawa, Badruddeen Tijjani Muhammad, ya ce NSCDC ta samu kiran agaji domin ceto yaran.

“Jami’in hukumar NSCDC na ƙaramar hukumar Buji, Abdulrashid Suleiman Adam ne, ya jagoranci aikin ceton yaran tare da kai su asibiti,” in ji shi.

Lamarin ya tayar da hankalin al’ummar ƙauyen, inda mutane da dama suka shiga miƙa ta’aziyyarsu ga iyalan yaran.

Hukumar NSCDC ta jajanta wa iyayen yaran.

Kazalika, hukumar ta ce tana ci gaba da bincike domin gano yadda lamarin ya faru.