Yara 33,000 za su ci gajiyar karatu daga gida a Katsina

Akalla yara ‘yan makaranta 33,000 ne za su ci gajiyar shirin karatu daga gida a Jihar Katsina. Wani shirin bunkasa ilimi mai suna ULS ne ya bullo da tsarin karatu daga gidan ga dalibai a jihar. Shirin, wanda ya samu tallafi daga Hukumar Kula da Ilimin Bai Daya ta jihar ta Katsina da kuma wani […]

Yara 33,000 za su ci gajiyar karatu daga gida a Katsina

Wasu yara kena da ke karatu daga gida ta hanyar rediyo

Akalla yara ‘yan makaranta 33,000 ne za su ci gajiyar shirin karatu daga gida a Jihar Katsina.

Wani shirin bunkasa ilimi mai suna ULS ne ya bullo da tsarin karatu daga gidan ga dalibai a jihar.

Shirin, wanda ya samu tallafi daga Hukumar Kula da Ilimin Bai Daya ta jihar ta Katsina da kuma wani asusun tallafa wa ilimi na kasa da kasa an bullo da shi ne domin daliban su ci gaba da karatu daga gida saboda zaman gidan da annobar COVID-19 ta tilasta.

Daraktan ULS a Arewacin Najeriya, Umar Farouk Bello ne ya bayyana hakan yayin wani taron horas da jami’an da za su koyar da daliban.

Ya ce shirin ya zabo mutum daya daga kananan hukumomi guda biyar daga kowacce mazabar dan Majalisar Dattijai, inda mutane 15 ke nan za su samu horon yayin da kowanne daga cikinsu zai horas da mutum 10 a karamar hukumarsa.

Darektan ya ce jami’an da za su samu horo kuma su ne za su wayar da kan yaran da kuma iyayensu a kan shirin karatun.

Kowanne daga cikinsu kuma zai zakulo iyalai 20 dauke da yara goma-goma da zai kula da su domin tabbatar da bayar da tazara a tsakaninsu.

Umar Farouk ya ce za a rika watsa shirye-shiryen ne a gidajen rediyo da talbijin na jihar ta Katsina da kuma kafafen sada zumunta irinsu ga iyayen da suke da sukunin mallakar manyan wayoyi.

Kazalika za a gudanar da gwaji ga daliban kafin da kuma bayan shirin wanda zai shafe tsawon makonni shida yana gudana.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos