Yara 5 sun mutu a cikin mota saboda rashin iska a Neja

An tsinci gawar yaran a cikin mota bayan iyayensu da makwabta sun shafe sa’o’i suna neman su

Yara 5 sun mutu a cikin mota saboda rashin iska a Neja

‘Yan Sanda a yayin bincike

’Yan sanda sun tabbatar da mutuwar wasu kananan yara biyar sakamakon rashin iska a cikin wata mota a garin Minna, Jihar Neja.

Yaran sun hada da mata hudu da namiji daya, ’yan uwa uku da wasu biyu daga iyaye daban-daban ciki har da dan mai motar.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya ce, ofishinsu da ke Kpakungu ya samu rahoto cewa an tsinci gawar yara biyar ’yan shekara biyar zuwa 13 makale a cikin wata mota kirar Honda Civic a unguwar Gurara Albishir da ke Minna.

Abiodun ya ce an gano nunfashin yaran sun shake ya dauke ne a cikin motar, bayan da iyayensu da makwabta suka kwashe awannin suna neman su.

Ya ce daga bisani aka sanar da ’yan sanda suka ziyarci wurin.

A cewarsa, rundunar ta gayyaci mai motar domin yi masa tambayoyi kuma ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Wata majiya a unguwar da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa, yaran sun yi kuskure ne suka kulle kansu a cikin motar wadda mai gidan ya yi watsi da ita sama da shekaru biyu.

Ya ce daga baya ne iyayen suka gano gawarwakinsu a cikin motar a ranar Lahadi da yamma bayan sun shafe sa’o’i suna neman su a unguwar.

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa