Yara 50m ke gararamba a titunan Najeriya —Gwamnati
Aƙalla almajirai miliyan 30 da yara marasa zuwa makaranta miliyan 20 ne suke gararamba a tituna a faɗin Najeriya
Gwamnatin Tarayya ta ce aƙalla almajirai miliyan 30 da yara marasa zuwa makaranta miliyan 20 ne suke gararamba a tituna a faɗin Najeriya.
Babban Sakataren Hukumar Kula da Ilimin Almajirai da Yara Marasa Zuwa Makaranta ta Ƙasa (NCAOOSCE), Dokta Muhammad Idris, ne ya sanar da hakan tare da jaddada buƙatar kulawa da su da kuma sama wa rayuwarsu alkibla ta gari.
A jawabinsa a yayin ƙaddamar da kwamiti da aka kafa domin sake fasalin ilimin almajirai na tsangaya, Idris ya ce, “baya ga koyon munanan dabi’u, mutane da dama suna cin moriyar raunin yara almajirai.
“Ba za a ƙara yarda da yanayin da yake haifar da barar yara a tituna ba.
- Mutum 182 sun mutu a hatsarin kwalekwale a Neja a shekaru uku —Bago
- NNPP na shirin amfani da kuɗaɗen ƙananan hukumomi a zaɓen Kano —APC
- Matar Gwamnan Akwa Ibom ta rasu
“Wannan batu ya shafi Najeriya gaba ɗaya ne, ba wani ɓangare na al’umma kaɗai ba.
“Almajirai da makarantun tsangaya yanzu suna da shugabanni da kungiyoyi daban-daban fiye da 2,000, wanda hakan ya sa gwamnati ta kasa hada su wuri guda.
“Shi ya sa gwamnati ta ga cewa ya zama wajibi a duba lamarin, da niyyar samar da koyarwar zamani gare su.
“Dole mu haɗa kai don share hawayen wannan ɓangare na ilimi da aka yi watsi da shi na tsawon lokaci,” in ji shi.
Idris ya kuma ɗora wa kwamitin alhakin haɗa kungiyoyin makarantun tsangaya da ke faɗin Najeriya a ƙarƙashin inuwa guda ta yadda za a iya zaƙulo da malamai masu nagarta daga cikinsu, da kuma yautata hulɗa da haɗin kai da Hukumar NCAOOSCE.
Idris ya ba da tabbacin da cewa da zarar an aiwatar da matakan da suka dace, za a iya haɗe kashi 60 cikin 100 na almajirai da tsarin ilimin tsangaya kafin saukar wannan gwamnatin.
Ya ba wa kwamitin wa’adin makonni uku don kammala aikinsu, yana mai ayyana cewa hukumar na tattaunawa da gwamnatocin jihohi don karɓar makarantun tsangaya da aka gina karkashin Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Kasa (UBEC) a zamanin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Da yake tsokaci, shugaban kwamitin, Sheik Sayyadi Alqasim, ya tabbatar da cewa za su yi aiki tuƙuru don ganin sun kammala aikinsu yadda ya kamata a cikin lokaci cikin inganci.