Yara 6,573 kawai ke yawon bara a Kano — Gwamnati
Hukumar ta jaddada cewa talauci, rashin aikin yi da kuma ƙarancin ilimi ne manyan dalilan da ke haifar da bara a jihar, ba wai yawan yara da aka nuna a rahoton ƙungiyar ba.
Gwamnatin Kano ta bayyana cewa ƙananan yara 6,573 ne kawai ne suke yawon bara a titunan ƙwaryar birnin jihar.
Hukumar Ƙididdiga ta Jihar Kano (KSBS) ce ta bayyana haka, tana mai ƙaryata rahoton wata ƙungiya mai zaman—Global Improvement of Less Privileged Persons Initiative (GIOPPINI)—cewa fiye da yara miliyan biyu ke yawon bara a Kano.
Daraktan Hukumar, Dakta Suraj Sulaiman, ya bayyana alƙaluman da ƙungiyar GIOPPINI ta fitar a matsayin “na bogi kuma marsasa tushe a cikin sahihan bayanai.”
Ƙididdigar KSBS ta nuna cewa mafi yawan yaran da ke bara a titunan birnin Kano matasa ne masu shekaru 11 zuwa 20, inda suka kai kaso 56.4 cikin 100. Yara ƙanana masu shekaru 0 zuwa 10 kuwa, ba su wuce 457 ba.
- ’Yan ƙungiyar asiri sun fille kan matashi a Bayelsa
- EFCC ta tsare El-Rufai, kotu da ICPC na jiran sa
Hukumar ta jaddada cewa talauci, rashin aikin yi da kuma ƙarancin ilimi ne manyan dalilan da ke haifar da bara a jihar, ba wai yawan yara da aka nuna a rahoton ƙungiyar ba.
Ta kuma zargi ƙungiyar da gudanar da bincike ba tare da izini ba, tare da umartar ta da ta janye rahoton cikin sa’o’i 48 ko kuma ta fuskanci matakin shari’a.
Rahoton Hukumar ya biyo bayan iƙirarin Daraktan GIOPPINI, Mohammed Ali Mashi, cewa yara miliyoyi suna kwana a wuraren da ba su da tsaro a cikin Kano.
KSBS ta amince cewa bara babbar matsalar zamantakewa ce, amma ta ce dole ne duk wata manufa ta dogara da sahihan bayanai.
Hukumar ta kuma tunatar da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya riga ya ayyana dokar ta-ɓaci a fannin ilimi tare da ƙaddamar da shirye-shirye na tallafa wa yara da matasa masu rauni.