Yara 70,000 na fama da karancin abinci mai gina jiki a Jigawa

An gano cewa babbar matsalar da ta fi addabar yara kanana a Jihar Jigawa ita ce karancin abinci mai gina jiki lamarin da ya sa ake samun yara tsumburarru. Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Jigawa ta gano cewa yara dubu 70 ne suke fama da ciwon yunwa kuma suke zuwa asibiti amsar magani mai sanya kuzari […]

Yara 70,000 na fama da karancin abinci mai gina jiki a Jigawa

An gano cewa babbar matsalar da ta fi addabar yara kanana a Jihar Jigawa ita ce karancin abinci mai gina jiki lamarin da ya sa ake samun yara tsumburarru.

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Jigawa ta gano cewa yara dubu 70 ne suke fama da ciwon yunwa kuma suke zuwa asibiti amsar magani mai sanya kuzari a fadin jihar.

Darakta a Hukumar Lafiya a Matakin Farko Dokta Muhammad Shehu Sambo ne ya tabbatar da haka a wata kasida da ya gabatar a wajen wani taron kara wa juna sani kan harkar lafiya da gyara muhalli da inganta yanayin tsaro a lokacin da ya wakilci Kwamashinan Lafiya na Jihar Jigawa Dokta Abba Zakari.

Ya kara da cewa babbar matsalar Jihar Jigawa ita ce rashin abinci mai gina jiki, kuma akalla yara 70,000 ne suke zuwa asibiti neman abinci mai gina jiki.

Ya ce karancin abinci mai gina jiki shi ne yake sawa yaran ba sa girma kuma hakan yana taimakawa wajen dakushewar kwakwalwarsu.

Ya ce Jihar Jigawa ita ce jihar da ta fi sauran jihohin Arewa karancin cutar kanjamau, inda ya ce hakan ya biyo bayan doka da Gwamnatin Jihar ta yi na hana daura aure a jihar sai an yi gwaji, sannan ya bukaci gwamnati ta yi wata doka da za ta sa masu cutar sikila da sauran cututtuka su ma su yi gwaji kafin a yi aure.

Da ya juya kan maganar rigakafin cutar shan-inna kuwa cewa ya yi kashi 93 na yaran Jihar Jigawa sun amshi allurar rigakafin, kuma yanzu a jihar babu cutar sai dai a shigo da ita daga wasu jihohi.