Yara 8 sun kone a hadarin mota a Yobe

A ranar Lahadin da ta gabata ce wani mummunan hadarin mota a hanyar Damaturu zuwa Gashuwa a Jihar Yobe ya yi sanadin konewar yara 8 kurmus sakamakon taho-mu-gama da motarsu Toyota Bas mai daukar mutum 18 ta yi da wata motar Golf.  Majiyarmu ta ce hadarin ya auku ne tsakanin Gashuwa da Bayamari a karamar […]

Yara 8 sun kone a hadarin mota a Yobe
Yara 8 sun kone a hadarin mota a Yobe

A ranar Lahadin da ta gabata ce wani mummunan hadarin mota a hanyar Damaturu zuwa Gashuwa a Jihar Yobe ya yi sanadin konewar yara 8 kurmus sakamakon taho-mu-gama da motarsu Toyota Bas mai daukar mutum 18 ta yi da wata motar Golf. 

Majiyarmu ta ce hadarin ya auku ne tsakanin Gashuwa da Bayamari a karamar Hukumar Bursari, yayin da Golf mai lamba dA 302 KAR, ta yi taho-mu-gama da Toyotar mallakar hukumar sufuri ta Yobe Line mai lamba 12 KGG dA a lokacin da direban Golf din ya yi ta kokarin shigar-sauri inda Toyotar ta kwace daga hannun direban ta gangara gefen titi nan take ta kama da wuta.
Wata majiya a babban asibitin Gashuwa inda aka kwantar da wasu daga cikin wadanda suka ji rauni ta shaida wa Aminiya cewa, galibin wadanda suka ji raunin kunar wuta ne.
Bulama Balau Bayamari yana daga cikin mutanen da aka yi jana’izar wadanda hadarin ya rutsa da su, ya shaida wa da Aminiya ta waya cewa, “kananan yara 7 da wata budurwa ’yar kimanin shekara 12 ne suka kone a hadarin kuma mun yi jana’izarsu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.”
Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin daya daga cikin manyan jami’an hukumar sufuri ta Yobe Line ya ci tura, amma direban motar Alhaji Madu ya ce hadarin ya faru ne da karfe 9:00 na safe a hanyarsu ta zuwa Gashuwa, kuma munin hanyar ya taimaka wajen aukuwar hadarin.
Da wakilnmu yya tunubi Babban Jami’in ’Yan Sanda na karamar Hukumar Bursari ta waya ya ce, a jiraya samu umarni daga sama kuma har lokacin aiko da wannan rahoton bai ce komai ba.