Yara biyu sun rasu a wani kududdufi a Kano
An yi kira ga iyaye su zama masu kula da ’ya’yansu ta hanyar sanya idanu.
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar wadansu yara biyu, Usman Nasiru dan kimanin shekara takwas da Nafi’u Ahmad, dan kimanin shekara goma a Unguwar Bachirawa ’Yan Rake da ke Karamar Hukumar Ungogo da ke Jihar Kano.
Yayin da yake yi wa Aminiya karin haske, Kakakin Hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi ya bayyana cewa hukumarsu ta samu kiran gaggawa daga wani mutum mai suna Sani Manaja inda ya shaida wa hukumar cewa yaran sun fada wani kududdufi da ke unguwar.
A cewarsa nan da nan hukumarsu ta aike jam’ianta da ke Rijiyar Lemo wadanda suka kware a wannan fanni, inda suka yi nasarar gano yaran biyu wadanda suke rai a hannun Allah, kafin daga bisani jami’an lafiya su tabbatar da rasuwarsu.
Ya bayyana damuwarsa game da yadda ake samun yawaitar masu mutuwa a ruwa a jihar inda ya yi kira ga iyaye su zama masu kula da ’ya’yansu ta hanyar sanya idanu a kan wuraren da suke zuwa tare da nuna musu illar sanya kansu a cikin wasu al’amura.
Kuma ya yi kira ga jama’a su yi hanzarin sanar da Hukumar ’Yan Kwana-Kwana game da duk wani abu da ya faru na hadari da ya hada da gobara da faduwar gini da hadarin abin hawa.
Ya kara da cewa za a iya sanar da su ta hanyar ziyartar ofisoshinsu da suke kananan hukumomin jihar 44 ko kuma ta hanyar lalubar su a wayar tarho ta lambobinsu.