Yara manyan gobe?
A kullum cikin ’yan shekarun nan, kai ko in ce tun lokacin da na mike a rayuwa nake jin ana cewa yara manyan gobe, ko kuma a dinga fadar ai ku ne matasa, lokacinku na zuwa, ku dai bi a hankali. Ba komai ke zuwa mini a rai ba, in na ga cewa kusan shekara […]
A kullum cikin ’yan shekarun nan, kai ko in ce tun lokacin da na mike a rayuwa nake jin ana cewa yara manyan gobe, ko kuma a dinga fadar ai ku ne matasa, lokacinku na zuwa, ku dai bi a hankali. Ba komai ke zuwa mini a rai ba, in na ga cewa kusan shekara da shekaru ke nan, amma yaran ba su zama manyan goben ba. Matasan ba su tasa ba, in kuma sun tasa, to, da alama, ba su tasa inda ya kamata ba ko kuma an tasa su gaba ne da matsaloli da wadansu abubuwa da ke hana musu sakat.
Mu duba da kyau mu gani. A yau wace rawa matasa ko yara suke takawa? A ina yaran suke ko kuma a ina matasan ke zama da rayuwa? Wannan tambaya ta neman sanin wai ina matasan Najeriya suke ne a yanzu, ma’ana, me ’yan shekara 20 zuwa 45 ke yi a kasar nan na ciyar da kansu ko kasa gaba, ina ga tana da muhimmanci da neman mafita domin a ga yadda za a shawo matsalolin da ke addabar yaran da matasan da kuma kasar da suke rayuwa a ciki. Ba wani abu ya jawo yin irin wadannan tambayoyi ba face ganin amon da yara ko matasa ke yi a farfajiyar ci gaban kasa ba abin ji ko gani ba ne.
Mu lura da kyau mu gani, yawancin fafutikar da ake yi yanzu a kasar nan tana ga ’yan shekara 45 zuwa sama ne. Yawancin shugabannin kasar yanzu tsofaffi ne ba matasa ba. Masu gudanar da harkokin tatttalin arzikin kasar, yawancinsu masu dattin hula ne ba masu dagawa ba. Haka sauran sassan rayuwa ta yau da kullum, cike take da tsofaffi, wadansu sun yi ritaya, amma sun kasa hutawa, sai fafutika da dingisawa suke ta yi, kamar yanzu suka soma rayuwa, tamkar matasa.
Daga cikin wadanda suke taka rawa yanzu wadansu sun yi shugabanci tun tale-tale, har yau kuma da su ake gwabzawa, duk da sun haye 60 ko 70 ko ma 80 a doron kasa. Wadansu kuma sun tara dukiya ta kin karawa, sun mallaki biliyoyin Naira ko ma Dala, sun kuma shafe shekara 60 ko 70 ko kuma 80, amma har yanzu bida suke yi, kamar yanzu suke soma rayuwa ko a ce su ma matasa ne ’yan shekara 20 ko kasa da haka. Haka yawancin aurarrakin da ake yi sai a ga cewa ba na matasa ba ne, sai dai wadanda sun taka sun haye, domin yawancin matasan, musamman wadanda suke a tsakanin shekara 25 zuwa 35, har yanzu ba su san inda kai ke musu ciwo ba, ba su ajiye ba, ba su ba wani ajiya ba. Yawancin yara da matasan ba sa maganar aure, in ma sun yi, ba mai amsa musu. Ga ’yan matan suna gani, suna son aure, amma abin ya faskara, domin ba su da abin hannunsu, bare su tara na aure ko daukar nauyin wasu can daban. Irin wadannan matasa har zuwa yau suna cikin gidan gandu, cinsu da shansu da makwancinsu da sauran lamurran rayuwa na hannun iyaye ko yayye. Su ne ke isar da sako ga iyayen ko yayye ta hanyar rubutu a bangon kofar gida, ‘a yi wa yaro aure ko ya lalace.’ In masu kula da lamurran nasa sun gani sun fahimci cewa yana bukatar aure su agaza in suna iyawa ko kuma su bar shi ya lalace ko ya lalatar.
A bisa irin wannan yanayi sai mutum ya fara tunanin, to yaushe yara ko matasan nan za su zama manyan gobe? Yaushe za su shiga cikin rigunan mulki da zamantakewa da ciyar da kasa gaba? Ba wannan ba ma, ina yaran matasan suke? Me suke yi? Idan har yau sama da shekara 40, yaran na nan yara, matasan nan sun kasa tasawa, to me muke tsammani zai faru nan da shekara 10 ko 20 masu zuwa, lokacin da yaran suka tsufa, matasan suka tsofe?
Amma kafin nan, shin ina yaran wannan yanki suke? Ina matasan namu suke? Me suke ciki? Ina manyan suke? Me suke yi? Yaushe za su kau wasu su karba? Tambayoyi ne masu rikitarwa, amma amsa su na da muhimmanci ga dorewarmu a matsayin dinkakkiyar kasa, mai shirin zaman lafiya da lumana!
Yaranmu har yanzu yaran ne, domin kuwa sama da miliyan 11 su ne ke galudiya da yawo bisa tituna a matsayin masu bara da maula da almajircin da bai fitar da A’i daga rogo. Yaran namu da ba sa bara ko roko ko watangaririya, suna can makarantun firamare da sakandare, suna ta fama da neman yin karatu cikin kunci da cin karo da yunwa da damuwa da rashin sanin makama, nan ma wasu gungu ne na kusan miliyan 10. Sauran matasan namu kuwa ’yan shekara 20 zuwa 30 yawancinsu har yanzu suna jami’a ko wasu manyan kwalejojin ilimi ko wajen bautar kasa, ba su gama karatun ba, balle su san inda kai ke musu ciwo. Wadanda sun gama kuma bautar kasa suke yi ba hidimar kasa ba, domin har yanzu cikin kangi suke. Nan ma wasu gungu ne da duhu suka sani ba haske ba. Wasu kuma daga cikin matasan namu, ba su nan, ba su can ne. Sun gama karatu, ba aikin yi, balle sanin makamar rayuwa. In ka tambaye su me suke ciki game da rayuwa, ba abin mamaki ba ne ka ji sun ce da kai, ‘ai rayuwa ta kare, muna jiran hijira ne zuwa ga Maiduka.’ Ga irin wadannan matasa, tsaka mai wuyar sha’ani ita ce abin da suka sani.
Ke nan, neman sanin inda yara ko matasanmu ke wanzuwa ba abin wahalarwa ba ne. Mun san inda suke, kama daga zauna-gari-banza zuwa ’yan tasha da banga da kauraye da masu shaye-shaye da ludu da madigo da karuwanci da sace-sace da damfara da ma duk wani ‘aiki’ da ya dace da yara da matasa a wannan zamani. Tambayar ita ce, irin wadannan yara ko matasa su ne za su kasance manyan goben namu ko kuwa wadansu za mu farauto daga wata nahiya su zama jagororinmu?
Za mu ci gaba.