Yara marayu sama da dubu 20 ke rayuwa a sansanonin ’yan gudun hijira
Hukumar Bayar da Taimakon Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA), ta tabbatar da cewa kananan yara marayu da ba su kai shekara 18 ba, sama da dubu 20 ne ke rayuwa a sansanonin ’yan gudun hijira da ke garin Maiduguri.Shugaban Hukumar SEMA ta Jihar Borno, Injiniya Satomi Alhaji Ahmed, wanda ya bayyana haka, ya ce […]
Hukumar Bayar da Taimakon Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA), ta tabbatar da cewa kananan yara marayu da ba su kai shekara 18 ba, sama da dubu 20 ne ke rayuwa a sansanonin ’yan gudun hijira da ke garin Maiduguri.
Shugaban Hukumar SEMA ta Jihar Borno, Injiniya Satomi Alhaji Ahmed, wanda ya bayyana haka, ya ce rikicin Boko Haram ya sa fiye da mutum miliyan biyu gudun hijira tare da shiga cikin halin kaka-ni-ka-yi da rashin tabbas a rayuwarsu, ciki har da kananan yara da suka rasa iyayensu da suke jibge a sansanonin ’yan gudun hijira kuma an kiyasta yawansu ya kai dubu 23.
Ya ce suna tsoron yaran su kamu da cutar yunwa saboda rashin samun isasshen abinci mai gina jiki duk da kokarin da gwamnatin jihar da ta tarayya da kungiyoyi irin su RED CROSS da UNICEF ke yi, wajen bayar da tallafin abinci da harkar ilimi. “Saboda haka muna rokon gwamnatoci da hukumomi da daidaikun mutane da kungiyoyin sa-kai na duniya su shigo don tallafa wa yaran don ceto su daga shiga mawuyacin hali,” inji shi.
Shugaban Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar, Dokta Sule Mele, ya ce irin yawan yaran da suka kamu da cutar yunwa a sansanonin ’yan gudun hijira 22 da ke garin Maiduguri, yana da daga hankali.
“Mun tantace mun samu yara dubu shida da suka kamu da cutar yunwa a sansanonin a shekarar da ta gabata. Akwai tsarin da muke yi kan yadda muke kula da yara da ke fuskantar wannan cuta ta yunwa, domin mukan ba su abincin da ya kamata, amma abin da muke fuskanta shi ne bayan sun fita daga wurinmu sun koma wurin iyayensu a sansanonin akan dawo da su cewa sun sake kamuwa da cutar saboda a ciki din ba sa samun abincin mai gina jikin da ya dace a bai wa yaro dan kasa da shekara biyar, kamar kunun gyada da waken soya da aka sarrafa da sinadarai masu gina jiki,” inji shi.